*RAYUWA TA THE NOVEL📔📖*
'''PART FOUR 4️⃣'''
*🅿️AGE 8️⃣*
'''GIDAN SU NUSAIBA.
Itace zaune cikin Dakin ta daukar wayarta tayi, Ta kira Nadia.
"Hello,
Nusaiba?
Nadia akwai Matsala...
Nusaiba Nima Abinda zan fada miki kenan akwai matsala.
Ok! Kizo gidan mu yanzu saimuyi magana toh, inji Nusaiba.
Nadia tashi tayi ta dauki mayafinta ta fito.
Gidan su Nusaiba ta tinkara kai tsaye.HIGHWAY.
Kenan Nusaiba Abinda zata fadamin kenan?
Amsar da zata bani kenan yasa fa kasa fadamin tin a jiya cewar tanada saurayi wanda takeso kuma zata aura.?
Salman shi kadai cikin mota yake ta tinanin sa.
Niyanzu ya zanyi kuma gashi nayi nisa a son Nusaiba, cireta a zuciyata lokaci daya bazai yuba.
Amman haka dole zan jure domin bazan shiga rayuwarta ba bayan da wani a ciki...
GIDAN SU NUSAIBA.
Toyanzu ke me kika yanke?
Nusaiba?Nadia shiyasa na tambayeki shawara izuwa yanzu banyanke komai ba.
Hakane! Kowannan su yanada kirki, kuma kowannan su abin aso ne.
Domin sanin irin yadda Muhktar yakeji a kanki hakan yasa nace zan shirya plan na cewar bakyajin dadi mugani ko zaizo.
Nadia yanzu mene Abinyi?
Nusaiba Kaina ya Kulle, idanna sami kaina a irin wannan halin kece kike fitar dani.
Yanzu na rasa me zance dake, But Ina ganin Ya Kamata ace ki saurari kowanne daga cikinsu.
Nadia kina nufin nayi irin kuskurenki? Na hada samari?
Look ba ina nufin haka ba, Nusaiba kowannan su aurenki yakeson yayi,
Abaya kinyi rayuwa da kowanne a matsayin Aboki.
Baki gama sanin halin kowannan su ba.
Ina nufin tinda rayuwar aure RAYUWA ce ta har abadah ki tsaya ki karanci kowannan su.
Ki kuma gani wane ne a soyayya yafi dacewa dake.
Inyaso daga baya sai muyanke hukunchi ni ina ganin hakan zaifi.
Gaskia ne wannan Nadia kinyi magana me kyau kuma wannan shine kadai zabina.
Kuma zanyi hakan.
Kincemin kema Akwai matsala mece matsalar?
Nusaiba Abu Adam ne ya kawoma su mama Naira Million 30 wai kudin aurena.
Cikin zaro ido da mamaki Nusaiba tace Miliyan Talatin? Wai shin meya maida kudine haka?
Nima bansani ba Nusaiba
Yace Nan da wata Biyu za'ayi auren,Innalillahi! Wannan wane irin rashin sanin ya kamata ne Toh Umma metace akai?
Nusaiba Umma tana cewa nayi hakuri na aureshi.
Yaya Nooratu kuma Alamunta na nuna tursasani nema.
Kuma babu wanda zai sani nayi abinda banaso.
A ah, kada kice haka Nadia mubi komai a hankali.
Nusaiba Su Umma sun manta da Abinda Lateef yayi mana a RAYUWA amman ni ban manta ba.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?