RAYUWA TA PRT 3 PG 9

8 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''🅿️ART  3️⃣'''

*PAGE  9️⃣*

'''WASHE GARI GIDAN HAJIA AMMIE.

Hidin dimu kawai akeyi taro ya kai taro.

Family din Dan Batta babu wanda baya wajen.

'Yan uwa da dangi da abokan arzuki kowa yana nan.

Aslam ne cikin Babban Parlour Shida Farooq da sauran Abokan su a bangaren Maza.

Suhailat kuwa tana tareda Ammie da kuma kawayenta suna Parlour suma.

Motar lateef ce tashigo cikin gidan Ammie.

Fitowa yayi tareda fadin Alhamdulillah  fito mana.

Nadia ce gaban Motar sa Itama Tasaka wasu kaya masu jarabar kyau.

Wani material ne me tsadan gaske amman kam dai babu Fara'a a fuskanta.

Dukda kasancewar tanason Lateef amman tarasa meyasa takasa samin kwanciyar hankali a tattare dashi.

Su Ammie suna ciki zanje wajen Aslam din zantayashi murna ki shiga koh?

Nadia dan murmusawa tayi tace tohh.

Sallama Nadia tayi tashiga cikin Parlourn gida na Ammie iyaye da 'yan mata kowa ana zazzaune.

Ammie ce tace zonan sirika ta zoki zauna nan.

Nadia cikin Fara'a ta kalli Ammie.

Gaggaisawa takeyi da kowa.

Ammie ce tace Jama'a kubani hankalin ku dan Allah zanyi wata 'yar sanarwa.

Wannan Itace Nadia, Kuma itace wadda babban jikana zai aura wato Lateef.

Kowa Fatan Alkhairy yakeyi musu da fadin Masha Allah.

Allah ya kaimu lokacin.

Nadia cewa Suhailat tayi Ina tayaku murna Suhailat.

Allah ya sanya Alkhairy.

Ameen Nadia nagode sosai.

Suhailat wani irin kyau tayi wanda nidai bazan iya misaltashi ba.

Gata fara wani haske ta karayi wanda saikace ba irin matan duniya dinnan ba.

Nida Ita da Suhailat dinma nakasa ganewa wayafi kyau.

Amman mubarshi Suhailat din kawai😉

Wai ina Khaleed ne kuwa kwana biyu banganshi ba.

Ayyaah khaleed yana bangaren Maza ai duka Har Aslam din suna cen.

Ok! Barina Ganshi. Nadia tashi tayi tafito.

Aslam ne yaketa karbar Allah ya sanya Alkhairy.

Kiran waya ne ya shigo wayar sa.

Wayar tana hannun farooq, Dagota yayi zai mikawa Aslam din Lateef dayake kusada Farooq dinne yaga Nadia ce.

Yadanyi zargin wani abu.

Hello,

"Hello inason Ganinka Aslam  Nadia ta fadi.

Nadia ai ina Gidan Ammie yanzu bazaiyu nafita wani waje ba.

"Nima ina gidan Ammie din ai, Aslam kafito wajen swimming pool ina jiranka.

Nadia kashe waya tayi Aslam tashi yayi yace excuse me do please.

GIDAN SU NADIA.

Wai Umma ina Nadia ta tafi ne?

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now