RAYUWA TA PART 5 PAGE 2

14 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''PART FIVE (5)'''

*PAGE TWO (2)*

'''OFISHIN NUSAIBA.

Zaune Take Itada Oga Muhktar Suna tattaunawa.

Nusaiba Haryanzu kinki kibani dama na aiko gidan ku?

Shin kodai bakya sona ne?

Nusaiba dan murmusawa tayi da fadin Ba haka bane Oga Muhktar kawai dai inaso mu kara fahimtar juna ne.

Kaga bamu dade ba sosai kadan bani lokaci...

Nusaiba tabbas bamu dade da fara soyayya ba Amman mundade tare ai.

Kinsanni na sanki mekuma kikeso kisani daya wuce wannan?

Suna cikin Maganar Wayar Tace tayi ringing, Salman ne ya kirata.

Kin dagawa Tayi saboda Oga Muhktar na wajen.

Kidaga mana ana kiranki?

No bawani abu Nadia ce kuma nasan bawani abu bane kawai kira tayi taji ya Office din yake.

Zan kirata yanzu..

Oga Muhktar tashi yayi tsaye, Ok Good, Nusaiba Da Gaske ina sonki.

Kuma burina shine aurenki, Dan Allah ki kara tinani akai..

Na koma Office.
Budewa yayi ya fita.

Dafe Kanta tayi tana tinani kafin ta dauki wayar ta kira Salman din..

"Hello"

Masoyiya Ta,

Na'am Nusaiba ta Amsa ma Salman.

Kayi hakuri ka kirani banyi picking ba..

"Haba ke kuwa nasan ai bakya kusa ne kokuma kina wani uzurin"

Ya kike ya yau fatan kina lafia?

Ehh Ina Lafia Lau Alhmdullh.

"Toh Masha Allah haka nakeso naji.

Dama kira nayi naji Lafian ki kuma tinda kina Lafia toh Alhamdulillah nima ina aiki ne yanzun"

Hmm Thom Nagode Kuwa,

"Idanna Danyi free zankiraki Muyi Maganah"

Thomm Shikenan babu damuwa.

"Sai Anjiman koh? Kikulamin da kanki".

Hmmm Thom ba damuwa.

Nusaiba bayan Ajiye waya Cewa tayi lallai Ina bukatar shawarar Nadia dole zanje wajenta.

GIDAN ALHAJI BASHIR.

Mahaifiyar Suhailat ce Hajia Fateemah tashigo dakin Suhailat din.

Kaca kaca dakin babu gyara!

Suhailat kwance take kan gado Kukan nan ne dai bata dainashi ba.

Mahaifiyar tace, tace Suhailat wai meyake damun kine?

Saboda namiji ya fita daga rayuwan ki duk kinbi kin rasa hankalin ki.

Kidubi dakinki fa?

Ke bakisan kaddara bane kome?

Suhailat batace da mahaifiyar ta komai ba.

Kinga Suhailat Saboda ke Mahaifinki yace na zauna a gida na wani lokaci na kula dake.

Amman jiya baki sauqo kasa ba yauma baki sauqo ba.

Suhailat ya kamata ki karbi kaddara Aslam ya rigada yayi aure,

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now