*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖
'''PART FIVE (5)'''
*PAGE NINE (9)*
'''GIDAN SENATOR I BAKO.
Hajia Ammie ce Tareda Duka 'ya'yan ta Sunzo yima Senator Ta'aziyya Akan Dansa Tahir daya Rasu.
Nagode sosai da sosai Hajia,
Naji dadin yadda kuka karramani haka kukazo da kanku ba aikeba.Ai Senator Wannan ba wani abu bane, kacancanchi mumaka fiye da wannan ba.
Duba da gwamnatin da takechi kunyimin nima abubuwa sosai.
Baka cancanchi nayo maka aiken Ta'aziyya ba da kaina ya kamata nazo cewar Hajia Ammie.
Nagode kwarai da gaske Rankishi dade Allah Ubangiji ya saka miki da Alkhairy.
Senator Ibrahim Bako Yake Fadi.
Securities ne ko ina ta gidan,
Amman yanzu Wane mataki zaku dauka akan wannan al'amari?
Ehh dazu Nayi Magana da AIG, kuma ya tabbatar min da cewa zasu kara tsaurara tsaro a kasa ta yadda duk wadanda sukayi wannan abu bazasu samu damar guduwa ba.
Ehh Hakane,
Dayake Ina cikin Wannan Hali na Jimami, Amman zamuyi magana dashi nima zuwa anjima inshaAllah.
Allah ya bayyana shi cewar Senator.
Ameen thumma Ameen Senator Inji Mahaifin Aslam.
Tashi sukayi don Tafiya, kara gaisawa sukayi domin yaji dadin zuwan Hajia Ammie.
Ammie itada Mutanen ta fitowa sukayi daga cikin gidan.
GIDAN SU SARAH.
Sarah ce Take waya da Lateef,
"Aina kusa dawowa, Karki damu ina dawowa bazamu kara sati biyu ba za'ayi bikinmu."
Hmmm Allah Kohh To Allah ya dawomin da kai lafia Ya Kai Mijina.
Nikaina A kage nake naga kadawo anyi bikinmu gani nakeyi kamar wata zata kwacemin kai inji Sarah.
"Hmm Kinaji Ninakine, kuma babu wadda zata iya kwaceni a gareki"
Haka suketa soyayyar su.
Radeeyah shigowa dakin tayi ta tarar da Sarah tana waya.
A zuciyarta tace Kigama Abinki wallahi saina Rabaku.
Fita tayi daga dakin.
KAN TITI.
Ammie ce take magana da Abdullahi.
Yanzu Ammie mene next move?
Abdullahi ka kwantar da hankalinka nasani bazaka iya hakan ba.
But try, Hankalinka a tashe yake ganin yadda abinda ya faru da Tahir.
Aslam dinmu yana raye kuma inshaAllah Aslam zai dawo kuma Allah zai tona asirin wadan nan da sukayi musu haka dukansu.
Abdullahi shiru yayi,
Abdul Mumin Da yake tuka motar ne yace Ammie Kina iya bakin kokarin ki.
Kuma inshaAllah Aslam zai dawo.
Hakane! Nima ta bangare na, ina bincike na.
Kuma inshaAllah zamuyi nasara babu abinda zai faru da Aslam.
Dpo Zaiyi Magana da Matar Tahir Zuwa Anjima Musaurareshi muji tukunnah Ammie ta fadi.
Shikenan babu damuwa Inji mahaifin Aslam.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?