RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
_( My Life )_'''PART SIX'''
*PAGE 1️⃣4️⃣*
_BAYAN KWANA BIYU.
PRIVATE HOSPITAL.Hajia Ammie ce Akan Gadon Asibiti kusa da Aslam.
Mahaifinsa yana tsaye.Aslam bude idonsa yayi, Ammie ya gani a kansa,
Sannunka da Tashi Aslam.Dan murmusawa kawai yayi mata, Mahaifinsane yace Ya jikinnaka?
Cikin Sassanyar Murya yace Da sauki Daddy.
Ammie ce tace kowa yana waje Amman mubiyu aka bama damar shigowa muganka.
Yanzu babu sauran Fargaba Komai yazama daidai yanzu babu abinda zai kara faruwa.
Kotu ta tura Murtala Mora gidan Kaso a bisa laifin daukar doka a hannu ta kisan Tahir.
Tsawon shekaru masu yawa.
Hawayene a fuskar Ammie tace sannan kai...
Fadamin Ammie inaji nikuma me?
Mahaifin sane yace duba da Alaqar da take tsakaninka da Tahir kuma kasan yayi wannan laifi ka goya masa baya baka tona masa asiri ba.
Kotu ta umarci da kaje gidan kaso na tsawon shekaru Biyu Kuma babu beli.
Mahaifin sa ya fadi cikin rashin jin dadi,
Hmmm Murmushi Aslam yayi yace Ni Wannan Hukuncin yayimin daidai.
Domin koba komai kacika maganarka Naja'atu tasami Adalchi.
Saboda haka wannan ba wani abu bane, Zanje Prison Zanyi shekaru biyu Wannan ma Experience ne na rayuwa Daddy.
Ammie kidena kuka.
Ammie ce tace Allah ya azurtaka da 'ya Mace.
Aslam wani murmushi yayi, ya tashi ina..ina take Ammie.
Ahalin yanzu Suna daki kaima bakada Lafia ka zauna ka huta kajiko?
A ah Ammie Inaso Naga Nadia Inaso Naga 'yata.
Aslam tashi yayi Mahaifinsa ya rikeshi cikin dingishi.
Ya fito.
Khaleed ne tsaye jikin kofar dakin da sauran Ahalin Ammie.
Aslam rungume Khaleed din yayi, Cikin Yanayi na shauki yace Kana bina bashi Khaleed.
Khaleed din da Bandage shima a jikinsa yace Kai Nawane BIRO Cikin tsokana.
Wuce yayi izuwa dakin da Nadia take,
Kwance take itada Jaririn Ta a gefe.
Ganin Aslam tayi zata tashi Aslam din cewa yayi kada kitashi koma ki kwanta.
Ya jikinnaki?
Ina lafia Mijina Ya jikinnaka?Ga 'yarka nan Bazaka dubata ba?
Cikin wani irin kallo yace, Nafi bukatarki akan kowa Nadia.
Ke kika kawomin ita dunia saina tabbatar kina lafia ne zan dubata itama.Nadia murmushi tayi yadda Aslam yake kaunarta haka.
Cikin kwalla ta rungumeshi da cewa zaka tafi ka barmu.
Murmushi yayi yace Haba kekuwa, Ki kaddara zanje neman Lafia ne kamar a baya.
Saboda Haka karki daga hankalinki, wannan ba wani abu bane Kuna zuciyata keda 'yar 'yarmu.
Shima rungume Nadia Matarsa yayi.
Sunan 'yarmu RABIA'AH.
Aslam yasawa 'yarsa sunan Ammie,
Nadia ce tace tabbas babu sunan daya dace da ita kamar na Ammie.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
Fiksi UmumLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?