*RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
_( My Life )_'''PART SIX'''
*PAGE 1️⃣*
'''BAYAGA DUK ABINDA YA FARU A CIKIN LITTAFIN RAYUWA TA PART 5, ASLAM YA TAFI KASAR WAJE SHIDA MAHAIFINSA DOMIN NEMO MAGANI A GARESHI.
NUSAIBA TAQI FUSKANTAR OGA MUKHTAR, YAYIN DA SARAH KUMA TA SANAR DA MAHAIFIN TA TAFASA AUREN LATEEF.
DOMIN JIN YADDA ABUBUWA ZASU KASANCE KUBIYOMU A RAYUWA TA PART SIX.
BAYAN WATA HUDU
(AFTER FOUR MONTH).GIDAN HON. ABU.
Abu Adam ne shida 'yan Jam'iyarsa suna tattaunawa.
Kaga Doguwa Ninasan babu wanda ya cancanta da wannan takara idanba niba.
Nine wanda ya rike mukamai kala kala. Cewar Abu Adam.
Bazamu dauki takarar gwamna guda mubama wanda bayada gogewa a siyasa ba.
Honourable Abubakar Adamu, baka rike wasu mukamai ba.
Kadaiyi senator kawai kuma bakada gogewa a siyasa.
Kasani fa Kujerar Gwamna Ba Abu bane da za'ayi wasa dashi.
Cewar Saminu doguwa.
Cece Kuce Aka fara inda shugaban Jam'iya yace Ya Isa.
Duna da cewar haryanzu basamu samar da matsaya ba dangane da Dan takarar Gwamna a jihar gwanaye.
Mundage wannan Zama na yau.
Sai zuwa sati na gaba.
Kafin zuwa wannan lokaci, Honourable Abubakar Adamu shine wanda Jam'iya tatsayar a matsayin Dan Takarar wannan Gari.
Wasu kam sunyi farin ciki wasu kuma sunata magana akam yaza Abama yaro matashi takarar Gwamna bayan baisan komai ba a siyasar ma.
Wasu Kuma suce ci bayane daga Senator ya dawo Gwamna.
Honourable Abubakar Adamu ne yafito zai shiga mota.
Saminu Doguwa ne yace dashi Honourable Har zaka wuce?
Abu Adam Kallansa yayi yace, Ko karna tafine Dan Iya?
A ah ni banace karka tafi ba, Allah ya kiyaye hanya.
Abu Adam mota ya shiga, yaronsa suka yana gaba.
Suka Asan Yadda Za'ayi da Saminu Doguwa domin yanaso ya bani matsala a tafiya ta.
Sa Aima megida Yau dinnan zakaji labari me dadi.
Cewar Suka.
OFISHIN SALMAN.
Nina Rasa irin wannan Abu Lateef, ace yau kusan wata hudu.
Abu yana faruwa, Ita Auntyn ta Bata kiraka Taji koma mene ba.
Shikuma Mahaifinta yamaki dawowa ayi magana ta fuskanta.
Lateef sauke numfashinsa yayi yace Salman na tabbata Don Mahaifinta baya kasar ne.
Da yana nan ninasan abin bazai kai har izuwa wannan Lokacin ba.
Lateef 4month fa ake maka magana Abu kara nisa akeyi.
Ai gwara kasanar dashi koda ta waya ne.
Inyaso Ya dawo koma ya yane ayi, Amman wannan ai bata lokaci ne.
Bata Daga Maka waya, sannan kuma Bata Duba Sakunan ka.
Wallahi Salman ban yaudari Sarah ba, Zan iya karbar laifin Ban sanar da ita abinda ya faru tsakanina da Radeeyah ba.
Kaga Ba saika rantsemin ba Nasan kafa Lateef.
Idan kai mayaudari ne tona sani kuma nima shine, Babu wanda zai fadamin Dabi'ar ka.
Yanzu mekacema Daddy dangane da lamarin?
Ehh kawai nabada Uzurin Mahaifinta yayi tafia ne Subashi lokaci ya dawo.
Nayi tinanin zan iya gyara komai kafin dawowar sa amman abin yaci tira.
Dole ya kamata mu sanar da Mahaifinta Gaskia this is very serious issue Lateef inji Salman.
GIDAN SU SARAH.
Radeeyah ce Tashiga dakin Sarah,
Yanzu ke duk tsawon wannan lokaci shikenan haka rayuwar ki zata kasance?
Saurayi ya yaudareki, kimanta dashi mana kawai..
But kusan watanni nawa kina abu daya kullun kuka kuka.
Sarah ce tace Radeeyah bakisan yadda nakeson sa bane.
Gaba daya rayuwa ta na rigada na bashi ita.
Na sallama masa kaina gaba daya.Radeeyah zama tayi gefen gadon Sarah tace.
Kinga Lateef ba mijin aure bane nasan yanzu kinsan hakan.
Tindaga Lokacin daya Sanar dani cewar ya dade yana sona, tinda ya fara ganina.
Nasan cewar shi mayaudari ne, Shiyasa kafin bashi Amsa saida na bashi hakurin yayi hakuri.
Bazan iya soyayya dashi ba, Domin koba komai Yana Tare dake.
Amman Mutumin nan Ya dagemin Akan Na yarda da bukatarsa, Dama shi Managing zaiyi dake.
Karna damu Yasan yadda zaiyi dake...
Danaga bazai hakura ba, shine na nuna masa na yarda har yacemin idanya aureki da wata Shekara Daya ko biyu nima zai aureni.
Aina Nuna Miki Chart din kin karanta.
Wallahi Lateef ba Mutumin Arxiki bane Sarah idanma zaki cireshi a ranki kici reshi kinjiko.
Allah ya baki Lafia.
Radeeyah ta fadi Sannan ta tashi ta fita daga dakin.
Sarah jitayi kamar Ansoka mata wuka.
Bakin ciki taji a ranta kamar zai kasheta...
GIDAN HAJIA AMMIE.
Kowa Yana Cikin Farin ciki kamar sallah.
Domin yaune Aslam zaidawo bayan watanni Hudu da yayi a Asibitin Kasar waje.
Nadia ce tasaka Wani Material dinta mai tsananin kyau kana gani basai Ance maka yanada tsada ba.
Hajia Ammie ma tasaka Atamfarta mai shegen kyau ga Zobunan ta nan da Sarka na Gold.
Mahaifiyar Aslam dinma Haka Kowa Alhamdulillah!
Alhaji RAUF da Alhaji MUmin Sune suka tafi dauko Alhaji Abdullahi da Kuma Aslam harda Doctor Din da Suka tafi dashi.
Nadia zaune Take Ammie ta hanata kowane Aiki tace ta huta saboda yanayin jikinta.
Horn Din Mota sukaji Me Gadi ne ya bude gate.
Inda Motoci Biyu suka shigo Daya Mustapha da Aslam da Doctor.
Daya Kuma 'yan uwa uku.
Su Ammie fiffitowa Sukayi Domin kowa yanaso yaga Aslam.
Bude Kofa Akayi Aslam ne yafito daga cikin Mota cikin nutsuwa.
Nadia Idonta Hawayene ya zuba inda taje ta rungume mijinta a gaban Kowa.
Aslam cewa yayi wace wannan kuma?
Nadia Zaro Ido Tayi Tace Ka Mantani?
Aslam Murmushi yayi mata da fadin Yazan Manta 'yar Matata.
Nadia Murmushi Tayi Masa da fadin Har Hankali na ya tashi.
Mushiga Daga Ciki Koh Fadin Mahaifin Aslam.
Wowww Alhamdulillah!!! Aslam Is Back Naji dadin wannan Lamari Mai Karatu Nasan kaima kaji dadin wanga Abu'''
_WRITTEN_
_BY_
_SYESERM_ ✍🏾✍🏾✍🏾
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?