RAYUWA TA PRT 1 PAGE 12

17 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL✍🏽📔*

_Page 12_

'''WASHE GARI.

DIAMOND UNIVERSITY.

Nusaiba kinji duka Abinda ya faru,

Nadia ce tareda Nusaiba inda ta sanar da ita duka abinda ya faru da kuma halin da take ciki.

Nadia Amman meyasaka Abu Adam yayi haka?

Nusaiba nima bansani ba, Yanaso ya rabani da kowa ne bayason na dinga kula kowa saboda wani kudiri nasa.

Tabbb, toyanzu ga abinda baba yace gashi kuma maganar Khaleed yaza kiyi dashi?

Nusaiba wallahi bansani ba shiyasa na sanar dake don idan kaina ya kulle naki bai cika kullewa ba.

Kibani shawara yazamu bulloma lamarin nan....

Nidai a ganina Nadia kawai kisanarwa da Khaleed din.

Wani irin kallo Nadia tayima Nusaiba da cewa kinsan me kikace kuwa Nusaiba?

Nadia yanzu fa Makama muke nema da zamu ruguza aurenki da Abu Adam duk abinda ta kama yi zamuyi.

Nusaiba ina tsoron abinda zaije ya dawo idan Baba yasan cewar ina kulla wani abu.

Nadia bamada Zabi ne dolene tasaka idan kuma zakiyi hakuri ki aureshi a haka tohh the choice is yours..

Dan Allah kidena fadin haka mana Nusaiba.
Cewar Nadia.

Nadia sannan duk yadda ake ciki kiyi gaggawar sanar da Lateef domin kada abu yazo yayi nisa.

Kekuma kirasa yaza kiyi a barki a ciki.

Numfashi Nadia tayi da kuma sauke kanta kasa tareda fadin,

Nusaiba haryanzu baice yana sona ba, tayaya zanje masa da maganar zanyi aure?

Kina ganin hakan ba cin fuska bane tinda nasan yana Sona?

Hmmm Nadia kenan bari kiji na fada miki, Ai lissafi ne abin.

Shi idan kika fada masa cewar mahaifinki aurar dake zaiyi indai har yana sonki da gaske lallai zai dawo domin bazai tsaya yana gani ayi auren ki ba.

Yanayin Yadda zaiyi tanan zakisan cewar lallai yana sonki ko akasin hakan.

Nadia Mufa so mukeyi dukta yadda za'ayi maganar aurenki da Abu adam ta kau

Inji Nusaiba.

Girgida Kanta Nadia tayi Alamun tabbas hakane...

GIDAN ALHAJI MUMIN.

Ammie ce zaune kan kujera itada Mama,

Suhailat ce ta fito daga dakin Khaleed din.

Zama tayi da cewar Nasamu yayi bacchi shine nace barina barshi ya huta.

Alamu sungwada An sallamo Khaleed daga Asibiti ne.

Allah sarki Suhailat allah ya baki lada yadda kike kulawa da Khaleed cewar Ammie.

Kinata dawainiya dashi Allah yayi miki Albarka.

Ameen ameen Ammie.

Ehmm Dama akwai maganar da nakeso muyi daku tinda dama kune kukasan halin da Khaleed yake ciki.

Mama ce tace Toh Ammie muna sauraronki.

Khaleed yana son yarinyar nan Nadia kwarai da gaske!

Munshaida Hakan, Banason cigaba da ganinsa cikin wannan halin.

Duk yadda za'ayi Inaso Ayi maza maza ayi bikinsu shida ita.

Yarinyar tanada Hankali, Nayaba da ita sosai.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now