*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖
'''🅿️ART 3️⃣'''
*PAGE 5️⃣*
DIAMOND UNIVERSITY.
'''Yanzu ina zan sami Aslam?
Nadia ta tambayi Nusaiba.Tinda Ance yana makarantar nan banajin akwai wajen da zaki sameshi daya wuce library.
Kaii, Na Manta da Library wallahi kunsan ya Za'ayi kujirani barinaje.
Ok! Nusaiba da Aysha Adam samun waje sukayi suka zauna.
GIDAN HAJIA AMMIE.
Ammie ai Magungunan ma sunkusa karewa,
Zara'u ce take baiwa Ammie magunguna.Ai gwara su kare Zara'u dama kullun sai ina uzuri ki dakatar dani wai lokacin shan magani yayi.
Hmm Ammie ai haqqi na nake saukewa likita yace indinga bakisu akan lokaci shiyasa duk abinda nakeyi hankalina yanakan baki magani.
Hmm Lallai kuwa ai ina gani Allah yayi miki Albarka,
Yaushe zakije gidane? Inason Mufita nayo miki siyayya sannan inason a kaiwa iyayenki wasu kayayyaki.
Ai Ammie saidai naje na dawo amman bazan iya tafiya ko ina na barki ba bakyajin dadi.
Hmm banda abinki Zara'u waye yakejin dadi yanzu?
Aikowa hakuri yakeyi.
Ammie da Zara'u Hirarsu suketayi.
DIAMOND UNIVERSITY
SILENT ZONE.
Aslam ne zaune Kan kujera Sanye da Medical Glass dinsa yana karanta littafi.
Nadia ce tashigo ta nufo izuwa inda yake.
Cire littafin tayi daga hannunsa tace mene matsalar ka?
Kallan ta yayi sannan yace kece matsala ta!
Mekikeyi Anan Nadia?
Aslam ba zuwa nayi muyi magana akaina ba akan abinda kakeyi nazo.
Aslam meyasa ne kake behaving haka?
Kowa yana cen wajen taron ku amman kai kana nan meyasa?Tukunna ma meyasa baka sanar dani cewar yaune Graduation dinku ba?
Banda abinki yaushe kika dawo Makarantar kawai bayada muhimmanchi kisanine shiyasa
Nima kuma
Bayada Amfani najene shiyasa nake zaune anan Nadia.Kuma idanma naje mezanyi?
Hmm, Nadia zama tayi kan kujera tace Kaga Aslam.
Nasan meyake damunka Amman yanzu Daddy yanacen kai yakeson gani.
Dan allah kaje ayi taron nan da kai kaima.
Banason Ganinka haka kaikadai anan.
Aslam kallan kwayar idon Nadia yayi yace Nadia tashi kitafi Dan Allah.
Kitafi kawai banason ganinki,
Aslam Kam yafara fahimtar kamar zai rasa Nadia ne yasa ya fara haka.
Rike Hannunsa tayi sannan tace Haryanzu ina Sane da Alqawarina Aslam Danni Kaje!
Aslam kallan ta yayi, yayi shiru.
Taso muje kaji.
Dukda yau ake taron kaddamar daku amman baka gaji da karatu ba.Harhada littattafan tayi ta ajiyesu wajen da ake ajiyewa.
Ta ce muje....
Nan suka fito Aslam kallan ta kawai yakeyi.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?