*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔
_Page 9_
'''WASHE GARI
DIAMOND UNIVERSITY.Tokinji Abinda yafaru.
Nadia ce tabama Nusaiba labarin yadda sukayi da Lateef.Hmmm Yadda kika fadamin kunyi waya dashi ya tabbatar da cewar Yana Sonki ne.
Kawai dai ya kasa fada miki ne yana dan jin nauyin yin hakan fadar Nusaiba.
Nusaiba nima na sani kuma na fahimci hakan tin kafin ya tafi.
Yana so ya fadamin Amman saiya fasa.
Nadia Shin Kina son Lateef?
Nusaiba ce ta tambayi Nadia.Nima bansani Nusaiba.
Hmm Kina Sonshi, Kinbani Amsa ai Nadia.
A wasu lokutan Amsar bansani ba tana nuna ba'ason mutunne domin idan kana son mutum kana iya fada masa.
Idan baka sonsa zakaji nauyin cewa baka sonsa domin abin yayi wani iri da yawa.
Sai ka bada amsar bansani ba, Shi mutumin zai fahimchi abinda kake nufi.
Amman sabanin hakan, Nadia a yadda yanayinki ya nuna da kuma yadda Lateef yake a wajenki.
Ni Nasan kina sonsa.
Nadia Kallan Nusaiba kawai tayi batace komai ba.
Nafahimchi yadda kikeji Nadia, Amman kibari Ya fara fada miki tukunna kafin ke ki fada masa koki Amsa masa.
Nusaiba mubar wannan maganar mushiga Aji.
Kyace a shiga aji ai tinda ana maganar soyayya.
Bahaka bane kawai dai Kar muyi late ne.
Tafiya Sukayi izuwa ajinsu.
GIDAN HAJIA AMMIE.
Ai ba mutunci ne da kaiba,
Na kiraka a waya kacemin zakazo.Nace a turomin kai kace zakazo
Kowa sai yace yana nemanka kaki kaje.Waikai mene damuwar ka kam?
Ammie ce itada Aslam zaune a Parlourn tana tsuyeshi.
Hmm Ammie kinsan yadda Wannan Al'amarin yake basainayi miki bayani ba.
Da Allah yimin shiru Anan, Kaidai Boko kamar kaika kawota duniya.
Saikace Akanka aka sauke bokon Gaba daya.
Kullun bakada Lokacin kowa.Kai kawai kanka kasani...
Ammie Dan Allah kifahimceni mana na kusa karasa karatun nan dai.
Kowa bayason wannan karatun nawa wai menayi ne haka?
Ba karatun kane ba'aso ba yadda ka tsara karatun kane ba'aso.
Bakada Lokacin Iyayen kama Mahaifinka yazo nan jiya shi yace rabonsa da kai tin wancen satin dayayi maka fada.
Akan baka zuwa Office.
Kai Aslam kakiyayeni Allah kaji na fada maka.
Dukanku Wallahi Abdul Lateef yafiku maida hankali akan Kasuwanci.
Mahaifinsa yayo dama, Amman shi wancen kullun babu lafia kaikuma kullun kana Makaranta.
Zan hadaku naci kaniyar ku Dukanku.
Kiyi hakuri Ammie za'a gyara inshaAllah.
Inji Aslam.Yanzu ma haka Makarantar zantafi amman saboda kiran ki shiyasa na biyo ta nan.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?