*RAYUWA TA THE NOVEL*
_Page 13_
'''DA DADDARE.
GIDAN SU NADIA.
Tabbb Amman Malam abin abin mamaki ne sosai.
Shaddodi guda biyar Yadika guda biyar da kuma Naira million daya ta dinki.
Wannan mata dai gaskia Allah ya mata arxuki.
Gaskia ne Asabe! Nikaina Tamatukar bani mamaki dukda ba abin mamaki bane idan akace itace tayi wannan kyauta dama ba yanzu ta saba yin irinsu ba.
Niyanzu wannan kudi Naira million Daya.....
Kinga kiramin Nadia cewar Malam Amadu.
Umma ce ta tashi tashiga dakin Nadia.
Nadia zaune take kan gadonta tana karatun Jarrabawa.
Babanki yana kiranki Cewar Umma bayan tashi tayi sallama.
Thom Umma bari nazo Nadia ta fadi.
Fitowa Nadia tayi sanye da Hijabi a jikinta sannan ta zauna.
Ah Nadia nace a kiramin kene don muyi wata magana dake.
Wannan kaya da kike gani...
Tukunna ma dai Nadia wane Khaleed?
Nadia tayi mamakin yadda mahaifinta yayi mata wannan tambayar.
Yama akayi yasan Khaleed din?
Baba Khaleed Amm!!
Kawai dai Abokinane haka cewar Nadia muryarta na rawa.
Hmmm Nadia Aboki fa kika cemin?
Dama tsakanin namiji da mace akwai abokan taka ne?Kayi hakuri Baba babu.
Yace yana sonane dama.
Kekuma wace Amsa kika bashi?
Baba banbashi Amsa ba haryanzu kasan cewar karigada kayima Abu Adam Alqawarin aure na.
Hakane!
Naji dadin yadda baki saba umar nina ba Nadia naji dadin hakan matuka.
Sannan Nadia wadan nan kaya da kike Gani Kakar Khaleed ce ta kirani dazu ta bani su.
Wannan Shaddodi ne Guda Biyar Sannan wannan kuma yadiddika ne gura Biyar.
Saikuma wannan Naira Million Daya ce tacemin Na dinka.
Bansani ba kokin santa ko baki santa ba.
Amman lallai babbar mata ce,
Nadia Khaleed dan gidan masu hali ne.Banason Matsala Daga gareni koke, Banason shiga jikin masu kudi.
Amman dazu Hajia Rabi tayimin maganganu sosai da sosai.
Hakan yasa nace idanna dawo lallai zamuyi magana dake donna sanar dake.
Ammm!! Nadia kisani bazan taba aurar dake wanda bakya soba.
Duk yadda nakai ga kaunar wanda nakeso ki aura idan har bakya sonsa nibazanyi miki auren dole ba.
Nadia Kije Kufuskanchi Juna keda shi, idan har yayi miki kina sonsa.
Banida matsala da hakan.
Idan baiyi miki ba Zan fada musu iya gaskia ta don babu abinda yawuce hakan.
Nadia Taji dadin yadda mahaifinta ya janye maganar sa akanta.
Yanzu ya bata dama akan lallai sai wanda takeso zai aura mata.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?