RAYUWA TA PART 4 PAGE 6

6 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL📔📖*

'''PART FOUR 4️⃣'''

*🅿️AGE   6️⃣*

'''GIDAN SU NADIA.

Juyowa Abu Adam yayi don ganin muryar wanda yace nine.

Lateef ne tsaye a bayansa.

Kai kuma meya kawoka Nan? Abu adam ya tambayi Lateef.

Waye kai da zaka tambayeni abinda nazo yi a nan?

Hmmmm!! Lateef kake kowa? Kanaji Wannan Ahalina ne, Kuma basa bukatar taimakon kowa tinda yanzu gani.

Ahalin naka daka tafi ka barsu bakasan Ahalin ka bane sai yanzu?

Umma, Zaku bar gidan nan....Inji Abu Adam.

Babu wanda ya Isa yasasu subar wannan gidan Cewar Lateef.

Hmm Abu Adam Murmushi yayi ya matso kusa da Lateef da fadin.

Lallai kasamu kanka, Malam Abdul Lateef Shine har nake fada kake fada.

Ka manta matsayina a wajen ka da kuma kasa baki daya.

Kasani idan har kasake ka kara kwazaroni tofa lallai zan batar da kai na har abadah.

Jimana Koda biron da nake Amfani dashi a Office dina baka isa ka batar ba ballan tana ni.

Nadia ce tace Lateef Ya Isa.

Abu Adam kallan ta yayi sannan yace Dama haka mukayi dake?

Bari kiji Nadia, Wallahi idan kika sake kikaci Amana ta Dake dashi duka sai kun fuskanchi baki na.

Cikin fushi Abu Adam yafito daga cikin gidan Ya Shiga Mota suka wuce.

Umma ce tace Ikon Allah, yanzu haka Abubakar din ya zama?

Yaya Nooratu ce tace Nima Tambayar da zanyi kenan Umma.

Nadia kuwa cewa tayi kayi hakuri,

Nadia wane Alqawari kikayi masa shin meyake fadane haka?

Kaga Karabu dashi bashida Hankali, surutan banza yakeyi.

Nadia!!!! Lateef ya fadi cikin Tambaya.

Da gaske Lateef babu komai.

Shikenan,

Kazauna Mana,
No, zantafi kawai Na dawo ko zuwa Anjima ne.

Shin kaji haushi ne abinda ya maka?

Nadia mubar wannan maganar kawai zan dawo da daddare na daukeki zamu fita.

Thomm, cikin murmushi Lateef ya fadi haka.

Umma Sai Anjiman ku saina dawo din.

Tohh Allah ya tsare Lateef, bamu gaisaba kuma.

Babudamuwa zandawo Anjima Umma fita kawai yayi Almu sungwada dai yaji haushin.

GIDAN HAJIA AMMIE.

Aslam ne shida Salman shigowar su kenan, Sunje Kamfanin Ammie dake Garin SULEJA.

Ammie ce tace Alhamdulillah! Tinda har kundawo Lafia.

Salman ne yace Ai Ammie sunji dadin zuwan domin kema sukaso kije.

Hmm Salman aini yanzu indai inadaku banida wata matsala.

Kowannan ku zai iya wakiltata a komai ba sainaje ba.

Hakane Ammie,
Yauwa Aslam. Yanzu kusamu kuyi wanka kuci abinchi koh.

No! Ammie ni yanzu zanje wajen Daddy ne yana jirana nace masa mundawo.

Ammie nikuma Lateef yacemin nazo yana Office dinsa kuma kinsan dama mundade bamu hadu ba so inaso naje na sameshi a Office din.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now