*RAYUWA TA THE NOVEL📔📖*
'''PART FOUR 4️⃣'''
*🅿️AGE 1️⃣3️⃣*
'''GIDAN SU SALMAN.
Lateef ne yashigo Har dakin Salman din,
Meyafaru kuma mezanyi maka? Salman ya tambayi Lateef.
Kaga Salman Bakamar yadda ka dauka bane, Mahaifin yarinyar nan kasani babu irin abinda baiyi mana ba.
NASANI! Amman ba'a yafiya ne?
Kasani lokacin da yayi mana abinda yayi mana nafika daukan zafi.Amman daga baya na hakura,
Kasani duk abinda za'ayi maka niyake fara batama rai kafin kai.Kasani rayuwa ba haka ake mata ba idan har kanason Abu dole saika zama me hakurin wajen samun wannan abin.
Kaga Lateef Yanzu kabani waje zan huta Dan Allah!
Lateef tsaye yake jikin bango, Shikenan taso muje zanje ya fadi cikin Amincewa.
Salman kallan sa yayi, Sannan yace idan dai har saboda na fada maka ne zakaje ni bazan je ba.
Nafiso kagane cewar kuskure kakeyi ka kuma fahimta da kanka cewar ya kamata ne kaje don kanason Sarah badon Maganganuna ba.
Hakane Abinda nazo na sanar da kai kenan zanje don nasan ya kamata naje kuma don Inason Sarah Salman.
Inji Lateef ya fada.
HIGHWAY.
Aslam ne shida Nadia Yashigo Quaters din gidansu.
Hmmm Toyanzu yaushene Bikin?
Bikin suwa Fa?
Nadia ta tambayeshi.Bikin mu mana?
Nadia girgida kanta tayi tace bikinku kaida wa?
Bikinmu nida Gimbiyata.
Tonikuma mezai hadani da bikinku kaida gimbiyar ka?
Nadia irin wasannan takema Aslam.Kinga wallahi Tallahi irin wannan wasan ma dagamin hankali yakeyi,
Dan Allah kibari,
Nadia daria tayi masa, Kaine kafiya gaggawa ai.
Dole Nayi gaggawa Nadia gani nakeyi kamar wani zai kwacemin ke.
Hmmm Babu wani wanda zai kwaceni, kaji koh?
Murmushi Aslam yayi mata, Inason muje Mugaida Umma fa.
Nadia shiru tayi kawai,
Meyasa kikayi shiru kuma?
Kawai banason Yin hakanne,
Kinga Nadia ba daidai bane Umma koba komai mahaifiyar kice,
Kuma bazataso duk wani abuda zai cutar dake ba nina sani badan kanta tace ki auri wanda bakya so ba.
Amman meyasa Yaya Nooratu take fadi Kuma Umma bata nuna mata cewar hakan bazaiyu ba.
Kinga Nadia Kishiga Mota yanzu muje Zamuyi magana Idan mukej Kuma ina mai tabbatar miki da cewa Umma zata fahimceki.
Nadia komawa mota tayi ta zauna, Don Aslam din ya matsane kawai.
GIDAN MALAM LIMAN.
Akaramakallah dama shine nace bari nazo na sanar da kai tinda dai Baba Kaine wanda ya bawa Amanar ita Nadia tin kafin ya rasu.
Tin kana waccen Unguwa.
Kuma ga wannan dan tago mashine nazo dashi Naira Million Uku ce babu yawa a dan jalabta.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?