RAYUWA TA PART 6 PAGE 3

7 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
          _( My Life )_

'''PART SIX'''

*PAGE  3️⃣*

'''BAYAN SATI BIYU.

PRIVATE HOTEL.

Wai Duk Tinanin Yarinyar ne haka?

Aslam ne tareda, Tahir cikin Hotel zaune.

Idan wani abu kake bukata Ga Sunan Su Meenah duka Babu wadda zaka nema tacema wani abu kotaki.

Amman akan yarinya daya duk kabi ka daga hankalinka.

Tahir Kallan Aslam yayi, Bakasan yadda nakeji akan Naja'atu bane Aslam.

Su Meenah bazasu taba zama gurbin taba, Besides ba irinsu daya ba.

Kaga Niyanzu taya zaka taimakamin akan issue din yarinyar nan?

Aslam zama yayi inda yace Kakira Bilkisu Muhadu da ita ayi Magana Kawai.

Yesss Hakane Kace wani Abu Cewar Tahir.

SATISFIED RESTAURANT.

Aslam ne Da Tahir Da Kuma Bilkisu.

Yanzu keme kike ganin ya kamata ayi?

Ehh Nidai Ina Ganin Ta bangarenta ba lallai a sami matsala ba.

Abu daya zamuyi shine kaje ka sami yayanta da maganar auren.

Inyaso, Shikenan Komai zaiyi daidai.

Hakane Bilkisu this is a very nice idea.

Babu damuwa kikace a ina yake koyarwa ma?

Saudatul Qur'an Wata Islamiyya ce nan Gaban gidansu.

Yana Koyarwa da Rana Da dare.

Ok Babu damuwa, Zamuyi Hakan.

Yanzu ita ya kukayi da ita?

Ehh Ita dai Ina Maka kokari a wajenta sosai, kuma Ita nunamin takeyi daga wajenta babu matsala yayan tane kawai.

Tokaga idan kagama da bangarensa shikenan indai ka tinkareshi da maganar za'ayi nasara inshaAllah.

Ok Good Job Bilkisu, Yanzu Ga wannan Kirike a hannunki, Duk yadda ake ciki zakiji daga gareni kinjiko.

Thomm Babu damuwa Yallabai.

Aslam Mu wuce inji Tahir.

RANAR ALHAMIS.

Dama Shine Nace Gwara Muzo Inyaso Saimu Nemi koda Ikon Zuwa wajen tane.

Tinda ita tace kaine, Mahaifi a wajenta.

Kuma koma mene saikanaso za'ayi.

Malam Murtala ne yace, Toh Alhamdulillah! Godia ta tabbata ga Allah.

A har kullun 'ya mace saita shiga cikin gidan mijinta shine rayuwarta ta cika.

Saboda haka ni ba sa Naja Zanyi a gaba na dafa na cinye ba.

Dole ko yanzu koba yanzu ba, Dama zatayi aure Darajar 'ya mace ce dama yin aure.

Saboda haka A matsayinka na wanda yazo kuma yake neman na bashi ikon Zuwa wajenta.

Na baka.

Saidai Nima Kuma Zannemi wata Alfarma a wajenka Domin da zarar ka aureta ko banida wani iko a kanta.

Wannan ba kamar yarjeje niya bace Alfarma ce nakeso kayimin.

Aslam Ne yayi Magana Yace Kome kakeson Fada Malam Murtala Muna sauraronka.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now