RAYUWA TA PRT 2 PAGE 4

10 0 2
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔

✨ _PART  2_  ✨

4️⃣

'''GIDAN SU NADIA.

Abu Adam ne zaune kan tabarma shida Mutane.

Gefe kuma Lateef ne shida Salman suma suna karbar wata gaisuwar.

Motoci ne sukazo kusan guda Hudu Mutane ne suka fito da 'yan sanda guda Biyu.

Suhailat ce ta fito daga cikin motar Inda Ammie kuma ta fito.

Khaleed ne yake tuka su Ammie din shima fitowa yayi daga cikin motar.

Mutane taruwa sukayi don mamaki mene Alaqar Hajia Rabi da Malam Amadu da tazo gaisuwar sa.

Hajia Rabi shahararriyar mai attajira ce Mamaki akayi akan mece Alaqarta da tazo gaisuwar malam Amadu.

Lateef da Salman ne sukaje suka gaisheta.

Lateef kana nan kenan?
Ehh inanan Ammie..

Toya hakurin kuma?
Hakuri da godia.

Allah yaji kansa,
Allah yay masa Rahma.

Ameen ameen Ammie.

Barina shiga ciki koh?

Thom Afito lafia Ammie..
Cikin Gidan suka shiga itada Suhailat.

Khaleed ne yazo ya zauna wajen su Lateef din.

Ya hakuri kuma?

Hakuri da godia Khaleed,

Allah yay masa Rahma.

Abu Adam ko kallan Khaleed ma baiyi ba.

Jiya nazo na tarar basanan.

Banyi tinanin wani abuba saida na kara dawowa da daddare shine yayar su take fadamin cewar ai suna Asibiti.

Aida daddaren ma ya rasu Cewar Salman.

Dan munbaro asibitin kenan kuma Nadia tayi mana waya Allah yayi masa rasuwa.

Allah sarki! Allah yajikansa.

Lateef cewa yayi, Ga dan uwanta ku gaisa mana.

Khaleed kallan Abu Adam yayi Abu adam dinma kallan Khaleed yayi.

Susun san sunsan juna!!!

Ya hakuri?

Abu kawai da Godia yace sama sama.

Alamu dai akwai wata a kasa.

Abu Adam duka haushinsu yakeji har Lateef din. Jira yakeyi a gama zaman makoki duk ya kora musu.

Babu su babu Nadia.

Cikin Gida Kuma Nadia ce jikin Ammie tanata bata hakuri.

Kidena kuka Malam Amadu Adduar ki yake bukata.

Ba kukanki ba.

Ammie yanzu banida kowa... Nadia take fadi cikin kuka.

Waya fada miki bakida kowa.

Kinada Mu kinji, Kinada mu.

Allah yaji kansa,

GIDAN ALHAJI ABDULLAH.

Zaune yake gidansa shida mahaifiyar Aslam.

Daga wayarsa yayi dacewa kai wai yaushe zaka dawo ne?

Daddy Nan da kwana biyu haka..

Shikenan Sirikinka ma ya rasu jiya da daddare.

Ya kamata ka dawo muje muyi musu ta'aziya.

"Innalillahi Wa'inna ilaihi raji'un Mahaifin Nadia ne ya rasu?"

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now