RAYUWA TA PART 4 PAGE 2

11 1 4
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL📔📖*

'''PART FOUR 4️⃣'''

*🅿️AGE   2️⃣*

'''POLICE STATION.

Khaleed ne Shida Ammie Sai Nadia a Police Station.

Hajia inshaAllah zamubi diddigin Lambar, Zamuga wanda yayi mata wannan message.

Amman Malama Nadia idan bazaki damu ba zan iya tambayar ki kuwa?

Dpo ya fada.

Ehh babu damuwa,
Malama Nadia shin banda Lateef dama baki taba yima kowa Alqawarin aurenki ba?

Babu, Shishi kadaine.

Nadia batace da Aslam ba.

Shikenan Malama Nadia idan muna bukatar wani abun zakiji daga garemu inshaAllah.

Babu damuwa Yallabai,
Amman Dpo Kana ganin wanda ya turo wannan sakon Nadia yakeso ko kuma Lateef din dama yake bukata?

Khaleed wannan sakon duka tsuhen turoshi Nadia ce.

Wanda ya turo wannan sako ina tabbatar da Nadia yakeso, bakuma yason Lateef ya aureta shiyasa ya fito da wata hanya daban.

Bamu tabbatar da hakan ba a hukumance amman ta bangarena ina tabbatar da hakan...

Amm!!! Dpo Yanzu mene Abinyi? Ammie ta tambaya.

Hajia Karku damu karku daga hankalinku.

Kamar yadda na fada zamubi diddigin lambar inshaAllah.

Zakuma mukama koma waye da yardar Allah.

Allah Yasa Dpo.

Gobene zaman kotu na Lateef wanda ya shigar dashi kara zaizo.

Na dauki lauyoyi tsayayyu don ganin Lateef ya fito.

Zamu saurareka Dpo fadin Ammie.

Shikenan Hajia a sauka Lafia.

Fitowa su Nadia sukayi itada Ammie da Khaleed.

Motar Nadia suka shiga duka.
Khaleed a gaba Ammie a baya Nadia tana tukawa.

Amman Ammie kina ganin Lateef zaifito?

Nadia Lateef zai fito ko shakka babu domin banga abinda yayi ba da za'a rikeshi.

Amman Ammie, ni Gani nakeyi Tinda Wannan Abu ya faru wanda ya shigar da wannan kara  yasan Lateef sosai.

Saidai abin shine Lateef baya rigima da kowa tayaya ne har aka shigar da kara a kansa.

Khaleed koma mene zamuji gobe kuma xamu ganshi da idonmu wanda yayi karar tasa.

Nadia kisaukeni a gida Koh?

Thomm Ammie,

GIDAN ALHAJI RAUF.

Elham ce kancinyar mahaifiyar ta Elham kanwar Lateef ce budurwa ce inda ta gama karatun ta na Jami'a itama.

Alhaji ne ya shigo ya tarar dasu,
Kara sowa yayi bayan yi musu Sallama.

Daddy ka dawo?

Nadawo ne na kara kwantar muku da hankali Elham.

Naje wajen Hajia dazu, ta kuma cemin Lateef yana cikin koshin lafia.

Tace yace yana gasheku ma, sannan gobene zaman kotu.

Wanda yayi karar sa zaizo.
Kuma zamuji hujjarsa nayin karar Lateef din.

Karku damu Mun zuba miliyoyi akan lauyoyi.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now