*RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
_( My Life )_'''PART SIX'''
*PAGE 6️⃣*
'''PRIVATE HOSPITAL.
Yanzu Abinda kikayi Kinyi daidai kenan?
Haba Nusaiba, Yanzu Ace da baiko a kanki ki kama hannun wani namiji.
Nibama zuwa wajen sane ya batamin rai ba.
Yadda kika rike hannunsa...
Nusaiba da Salman ne a Reception suke magana.
Dan Allah Salman Kayi hakuri, Nasan kaime fahimta ne kuma zaka fahimceni.
Nusaiba na fahimceki ame?
Koda yaushe da haka kike rufemin baki Ai zan fahimceki, Haba Nusaiba Wannan fa Magana ce ta rayuwa ta.
Kinsani Nasani ba daidai bane yin hakan, Ok Ame zan fahimcekin?
Nusaiba Kallan Salman tayi cikin Nutsuwa da tattaro hankalinta izuwa gareshi.
Cikin kwayar idonsa ta kalla, Salman kai kadai nakeso.
Kuma kasan kaine wanda nakeso, kuma nakeson na aura.
Dan Allah kadaina daga hankalin ka akan kananan abubuwa.
Salman bazan tabacin Amanar kaba, A halin yanzu Oga Muhktar yana bukatata ne.
Shin kanaso Ace Sanadiya na wani ya fara shaye shaye?
Ace saboda rasani wani ya shiga mummunar rayuwa.
Nusaiba awajen kine wannan yake karamin abu amman ba a wajena ba.
Hannunki fa Nusaiba, Hannunki? Haba Mana....
Ok! Wato Saboda ya fara shaye shaye Shine yake bukatar ki Wato ni bana bukatarki.
Bikimin Adalchi ba da kika fadi haka, Amman Babu komai Nima zan fara shaye shayen ko kuma na barki tinda kinsamu me shaye shayen kuma kinfi son me shaye shayen.
Salman ya fadi ya kauda fuskarsa.
Nusaiba Juyoda fuskarsa tayi, Ka kalli cikin idanun Salman.
Son kane kadai a ciki, bandashi babu komai.
Salman kaine kadai gaskia ta, Dan Allah kadena fadin zaka shiga Mummunan rayuwar nan banason jinta daga gareka.
Kayi hakuri, Bazan kara ba inshaAllah.
Dan Allah Salman kamar yadda kasaba fahimta na.
Inason ka kara bani wata damar, Wannan shine na karshe.
Inaso Oga Muhktar Ya Samu Kansa ya kuma koma rayuwar sa da yakeyi a baya.
Dan Allah, Sannan Nagode da taimaka min da kayi wajen kawo shi Asibiti.
Salman Kallan Nusaiba Yayi Cikin idonta.
Ina sonki Nusaiba, Ina Matukar Kaunarki, Ina Miki Irin Sonda ban tabama wata 'ya mace ba.
Ina Kishi akanki don ina sonki.
Dan Allah, Kidinga tina Wannan A koda yaushe.
inshaAllah Salman, Nima Kuma Ina Kaunar ka.
Nagode sosai.
Karki damu ninayi masa ne don Allah kawai.
Amman Ya akayi kasan ina gidansa?
Naje wajenki a Office naga fitowarki da mota shine na biyo bayanki.
Likita ne Yazo Yace Muje Office dinko?
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?