*RAYUWA TA THE NOVEL✍🏽📔*
_Page 8_
'''DIAMOND UNIVERSITY.
Meyasa kaimin haka Khaleed?
Nadia ce take tambayar Khaleed.Nadia Kiyi hakuri Amman bazan boye miki ba tabbas ina kaunar ki.
Ina Sonki ba kadan ba Nadia.
Nadia Kallan Khaleed tayi, Meyasa kadaukeni kakaini Wajen Ammie baka sanar dani cewar zaka kaini a matsayin wadda kakeso?
Khaleed idan inada wanda nakeso Fa?
Nadia Bakida wanda kikeso, Idan kinada wanda kikeso a dan dadewar da mukayi da kuma sabawar da mukayi Tabbas zansani.
Dan Allah Nadia kimin Wannan Alfarmar Domin bantaba Soyayya ba bansan yadda akeyi ba.
Wallahi kece mace ta farko wadda nagani kuma naji inason kasancewa da ita.
Nadia Shiru tayi,
Dan Allah Nadia, Kifahimchi yadda nakeji.
Khaleed bazan iya Amsa maka cewar ina sonka ba, A halin yanzu.
Amman kabari zanyi tinani hade da shawara.
Nadia Amsarki Guda daya ce Idan batazo a Ehh ba zatazo a yin shiru.
Duk wadda kika bani Zangode miki nakumayi Amfani da ita.
Khaleed Motarsa yashiga Sannan Yace Nagode.
Taka motarsa yayi ya wuce,
Tabbbbb, Nadia Gaskia abin nan ya bani mamaki Makura.
Kingafa Matar nan Dubu Dari Dari daga zuwa gaisheta bamuma san cewar zamuje ba.
Nadia yanzu tayaya ne zakice bakyason Khaleed.
Nusaiba inajin Tausayin Khaleed ne kawai, ina kumajin tsoron furta masa cewar bana sonsa.
Rashin Lafiar sa yana tashi ne lokacinda yaji ko yaga abinda bayaso.
Nusaiba Dan Allah kibani Shawara wallahi kaina ya rufe gaba daya.
Hmm Nadia Nima yadda kika fada hakanne, Amman yanzu dole muci gaba da lallaba Khaleed.
Musamu har lokacinda zamu iyayi masa bayani ya fahimta.
But for now banajin shine lokacin daya dace.
Amman wai mene ma laifin Sane?
Ni ina ganin ma da kin Amince masa Nadia.Khaleed bashida wani aibu ai mutunne mai hankali sanin ya kamata da kuma barkwanci.
Cikin wani irin kallo Nadia ta kalli Nusaiba da fadin Kinsan me kike fada kuwa?
Kenan ya sunana Idan nayi haka Nusaiba kinsani cewar Abdul Lateef Yana sona.
Nadia kema cewa kikayi Yana sonki shin ya furta miki ne?
Ba wannan ba ke kina Sonsa?
Nusaiba Ehh Inason Abdul Lateef, Sosai Kuma ba kadan.
Nusaiba Naira Biyar dinda Lateef ya kashemin tafi wannan dubu darin sau dubu dari a wajena.
Nadia Amman baki sanar dashi ba shima kuma bai sanar dake ba harya tafi.
Nusaiba Hakane bamu sanar da juna ba, Saboda shi yana tsoron sanar dani nima ina tsoron yin hakan.
Uhshhh, Sauke numfashi Nusaiba tayi sannan tace, Kunyi Magana dashi.?
Salman yace idanna koma gida na kirashi Lateef din ya bashi sako ya kawomin.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?