RAYUWA TA PRT 1 PAGE 11

13 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL✍🏽📔*

_Page 11_

'''THE NEXT DAY.
           GIDAN SU NADIA

Shiyasa Nace Ta turomin kai don Samin tabbacin inda ta sami wannan kudin.

Mahaifin Nadia ne Shida Aslam da Nadia.

Baba Hakane Nine Na bada Wannan kudi,
Kuma Naji Matukar dadi sosai da Har kanemeni donjin yadda akayi Nadia ta sami wannan kudin.

Hakan yana nunamin cewa lallai Nadia Yarinyace wadda aka tsaya a kanta sosai.

Inji Aslam.

Hakane Malam Abdul Salam, Tabbas Nadia koda Naira daya na gani a tattare da ita saina bibiya.

Hakan yasa da aka kawomin kudi akace dan makarantar sune nace ta turomin shi naji ta bakinsa.

Gaka kuma kayimin bayani Saidai Malam Abdul Salam Wannan Kudin Sunyi Yawa.

Ina Ganin Bawa mace irin wannan kudin Haka, haka kawai zai jawo maganganun.

Bawai zan maida hannun kyauta bane Amman Dan Allah Ga kudin nan ka koma dasu.

Fadar Mahaifin Nadia, Nadia tana zaune Uffan Batacewa.

Baba Idan kace na koma da wannan kudin nima bansan mezanyi dasu ba.

Tana iya yiwuwa Naje ba kashe su wani waje kuma akan abinda nasan bazai amfaneni ba.

Baba Wannan kudin dana bayar sunrigada sun fita daga wajena babu su a lissafi na.

Koda ace yanzu na fita daga gidan nan da kudin nan Kafin naje gida zan badasu.

Saboda Haka baba kayi wannan Alfarmar Ka bar wannan kudi Idan kaimin haka toni zanji dadi matuka.

Girgida Kansa Mahaifin Nadia yayi kusan mintina Biyar,

Baice komai ba.

Shikenan Malam Abdul Aslam,
Mungode kwarai da gaske Allah ya saka maka da Alkhairy.

Ameen ameen Baba wannan Adduar itace kadai abinda nakeso a gareka.

Masha Allah, Zanci gaba da maka Wannan Adduar Allah ya bada Sa'a a karatunku baki daya.

Ameen Ameen Baba cewar Aslam.
Nixan koma yanzu Dan daga makaranta ma nake tace kana nema na.

Toh toh! Allah ya tsare Allah ya kiyaye hanya.

Tashi Aslam yayi Yafita bayan sunyi Sallama da Mahaifin Nadia.

Nadia ce ta biyoshi Har wajen Motar sa.

Kallan sa tayi tareda cewa Kayi hakuri da yadda mahaifina yayi maka Tambayoyi.

Haka yake, Ina fatan Zaka fahimceshi.

Hmmm Nadia kenan, Karki damu Ni naji dadin hakan ma.

Hakan kuma ya tabbatar min keba macece wadda zatayi abinda ranta  yakeso ba.

Naji dadin yadda mahaifinki ya tsaya a kanki wajen tarbiyar ki.

Allah Ya kara masa Lafia Nadia.

Ameen Ameen Nagode Sosai Aslam.

Kema Allah Ya kara sauqi,
Hmm Ni ai na warke Gobe ma zaka ganni a makaranta.

Daria Aslam yayi tareda cewa Thom Allah ya kaimu

Sai Anjima nima barina koma Makarantar.

Shiga Motarsa yayi, yayi tafiyarsa Abinsa.

Wayar Nadia ce take Ringing Dagawa tayi dacewa Hello.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now