RAYUWA TA PRT 3 PG 1

13 2 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''🅿️ART 3️⃣'''

*PAGE 1️⃣*

'''BISMILLAH ARRAHMAN ARRAHIM.

BAYAGA DUK ABINDA YA FARU DA NADIA TSAWON LOKACI MAI YAWA BATA A HAYYACINTA.

YANZU KIMANIN SATI BIYU DA FARUWAR AL'AMURA TSAKANIN NADIA DA 'YAN UWA GUDA UKU.

ANSAKI ABU ADAM YATAFI BABU WANDA YASAN INDA YAKE, NADIA TA DAWO GIDAN SU TACI GABA DA RAYUWA.

MU KAFTA!!!

RAYUWA TA! RAYUWA TA!! RAYUWA TA!!!

GIDAN SU NADIA.

Khaleed ne inda tsaye kofar gidan, Nusaiba ce ta fito.

Sannun Khaleed.

Yauwa Nusaiba yakike ya garin?

Lafia lau Khaleed yasu Ammie kuma?

Ammie tana Lafia lau.
Nadia fa ya jikinnata?

Khaleed Nadia dai gatanan jiki Alhamdulillah zamuce.

Amman ni gaba daya ba Nadiar dana sani bace.

Akoda yaushe batada magana Saita Aslam!

Khaleed ne yace Innalillahi Wa'inna ilaihi raji'un!

Wato Nusaiba ina cikin damuwa Sosai, Bansan meyake faruwa dani ba.

Gaba daya banida sukuni a rayuwa ta.

Allah sarki Khaleed, Aiba kaikadai ba.

Mukanmu Nadia gaba daya ta canja mana.

Yanzu kusan Sati Biyu kenan da komawa Makaranta Amman haryanzu Nadia bata fara zuwa ba.

Ni tsoro nake kada wannan lalurar tataba karatun ta wallahi.

Nadia bata wasa da karatu amman yanzu Nadia tamaki yadda cewar tana zuwa Jami'a.

Khaleed shiru yayi yace Yanzu haka za'a zuba mata ido kenan Nusaiba?

Nitamaki So ta ganni...

Ta manta dani gaba daya tace ita bata sanni ba bata taba rayuwa dani ba.

Khaleed kayi hakuri, ba kaikadai bane.
Nikaina yanzune tasaki jiki dani.

Da Umma kadai ta yadda domin itace take biye mata a komai.

Nusaiba zanyi magana da Ammie, Gaskia bazamu zuba mata ido haka ba.

Dole a fita da ita koda kasar wajene don nema mata lafia.

Nusaiba cewa tayi Gaskia dai Nadia tana bukatar tina Rayuwarta ta baya.

Don hakan yanada Matukar muhimmanchi a gareta.

Babu damuwa Nusaiba niyanzu zankoma inshaAllah zanyi magana da Ammie akan hakan.

Shikenan Khaleed mungode kaji Allah ya saka maka Da Alkhairy.

Ameen ameen babu damuwa ki gaida su Umman Nusaiba!

Sallama Sukayi Nusaiba ta shige cikin gidan inda shikuma ya shiga motarsa ya wuce.

GIDAN ALHAJI BASHIR.

Aslam ne ya shigo da motarsa inda yayi parking ya fito.

Shigowa yayi tareda Sallama,
Mahaifiyar Suhailat ce zaune kan kujera sai Halima akan Carpet.

Durkusawa Aslam yayi har kasa inda ya gaisheda Maman Suhailat.

Yasu Maman Naka?

Suna lafia lau Mommy,

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now