RAYUWA TA PRT 1 PAGE 10

15 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔

_Page 10_

'''WASHE GARI.

DIAMOND UNIVERSITY.

Nusaiba ce zaune Itada Aysha.

Assalamu Alaikum Khaleed ne yayi musu Sallama.

Cike da Murmushi a fuskarsa Yace  Barkanku da Wannan Lokacin.

Khaleed kaine Da Safe haka a makarantar tamu? Nusaiba ta tambayeshi.

Nine Nusaiba Ya karatun kuma?
Karatu Alhamdulillah! Gashinan muna fama.

Masha allah, Ina Nadia Fa?

Nadia batazo Makaranta ba yau batadan jin dadi ne.

Innalillahi Wa'inna ilaihi raji'un cikin tashin hankali Khaleed ya fadi haka.

Karka wani daga hankalin ka dan likita yace Ta huta nema amman da zatazo makaranta yau.

Nusaiba karna daga hankali na fa kikace kuma kinyi maganar likita yanzu.

Ehh Maunje Asibiti ne kawai an dubata kuma Anbata magunguna
Amman da sauqi ai.

No! No! Dole ina bukatar na ganta Nusaiba.....Cikin Damuwa Inji Khaleed.

GIDAN SU NADIA.

Nadia ce cikin daki gari yayi mata zafi takasa komai tinjiya da daddare.

Umma ce tashigo dakin da cewa Yaya Jikinnaki?
Umma Jiki Na yayi sauqi.

Amman kina cikin damuwa Nadia,
Umma Maganar Baba ce Akan Cewa da yayi yaba dani wa Abu Adam.

Umma Baba bai tambayeni ko ina sonsa ba ko bana sonsa.

Nadia mahaifinki ya yanke wannan hukuncinne don sanin cewar abinda yakeso shine kikeso.

Abinda yasa bai tambayi shawarar kiba don yasan cewar kema zakiso hakan ne.

Amman Umma nibanason Abu Adam kema kinsani.

Nasani Nadia Nasani! Amman yanzu bazaiyu kai tsaye mutin kari mahaifinki da wannan maganar ba koni koke.

Dole ya kamata mujira.

Umma mujira har zuwa yaushe har sai anzo ansa rana Umma?

Kinga ki kwantar da hankalin ki, yace ya bashi kenan a matsayin wadda zai aura.

Bawai ya Aura masa ke bane kisani komai na iya canjawa cikin kankanin lokaci.

Abu Adam bazai aure kiba har sai kinason hakan, idan bakyaso mahaifinki bazaiyi miki auren dole ba.

Sannan Nadia Kidena saka damuwa a zuciyar ki kinjiko?

Komai zaiyi daidai inshaAllah.

Nadia shiru tayi tana sauraron Umman,

Allah Yasa Umma, Fadar Nadia.

Cikin Gidan Aka shigo Bayan yin Sallama Muryar macece.

Bari naje na duba Nadia.

Fitowa Umman Tayi da cewar wai kece banason Shakiyanci gidan bakon kine?

Nooratu ce Babban 'yar mahaifin su tazo gidan.

Domin ta dade batazo ba, itama tana fama da rayuwa ga mijinta itama babu lafia tana jinyarsa a gida.

Umma ai cewa nayi bari mugani zaki gane wace cikin daria fadar Nooratu.

Shigo Ciki Mana, inji Umma.

Sanninki da zuwa Noora Ya gidan kuma ya me gidan?

Lafia qalau Umma, Jikin dai gashi nan sai godiar Allah.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now