RAYUWA TA PRT 2 PAGE 10

6 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔

✨ _PART  2_  ✨

🔟

'''Fitowa Lateef yayi daga wanka inda yaga Salman din tsaye yana Kallan wayarsa tana ringing.

Kanaji wayana yana ringing shine bazaka daga kace bana kusa ba ka tsaya?

Salman kallansa kawai yakeyi...

Na tsaya ne ina tinanin wa kake yaudara tsakanin Nadia Da ita Sarah.

Lateef cikin Mamaki yace Sarah kuma bangane me kake nufi ba Salman.

Mtsww Kaga Lateef wannan wasan naka yazo karshe kajiko.

Karka wani nunamin bakasan komai ba kajiko.

Haryanzu kuna tare da Sarah Amman nida 'yan uwanka koda yaushe nuna mana kakeyi kunrabu.

Kuma bakasan duk wata Alaqa tsakaninku, meyasa kakemana karya?

Lateef ne Yace nifa bangane mekake fada ba Salman.

Kagane Mana Lateef kada ka rainama kanka wayo mana.

Sarah ce ta kiraka yanzu, bazata kiraka ba sai da izininka zaka cemin bakasan da hakan bane.

Salman wallahi bansan Sarah zata kirani ba sannan ni banida wata Alaqa da ita kasani cewar munrigada munrabu kusan 2yrs kenan yanzu.

Kaga Lateef Sarah ta kara dawowa cikin rayuwar ka nasani kada ka boyemin komai.

Sannan wannan Heart din da yake kan sunanta shima bakasan dashi ba koh?

Lateef daukan wayarsa yayi yace Wallahi Tallahi kaji na rantse maka Bansan yadda akayi Lambar Sarah tashigo wayana ba.

Banida ita kuma itama batada tawa idanma tanada ita bansan inda ta samu ba.

Wallahi Da gaske nake!

Hmm Lateef kenan Baka shirya fadamin Gaskia bane shikenan kawai manta da wannan maganar.

Lateef kam shiru yayi daga wanka ya fito dukda dakin akwai Ac da fanka Amman harya fara hada gumi.

Salman ne yace wannan gumin kuma da kakeyi fa?

Ni nima bansani ba, kazo ka titsiyeni ya bazanyi gumi ba Salman?.

Shikenan ya isa, ina zamuje Yanzu daka kirani.?

Eh inaso muje Station dinnan ne wajen Dpo maganar Nadia.

Ok shirya toh cewar Salman.

GIDAN ALHAJI BASHIR.

Suhailat ce kan kujera ta dora kafarta a kan table.

Tanashan Flavor Mai Sanyi Abinta tana daddanna waya.

Halima ce tazo ta zauna kan carpet inda tace Aunty Suhailat yayi miki yadda kikeso?

Suhailat kallanta kawai tayi tace Baimin ba tashi zanyi naje na zubar!

Halima Murmushi tayi.

Yauwa Halima Dukda ba wani Hankali gareki ba dai Amman barina tambayeki wata shawara.

Thomm Aunty Suhailat.

Halima wai da farko tayaya ne zaka gane cewar Namiji yana sonka?

Aunty Suhailat Akan Ya Aslam ne koh?

Kinga banason shegen munafurci kinjiko Abinda na tambayeki daban Tambayar kuma da zakimin daban.

Idan bakida Amsa kitashi kitafi karki batamin rai Da Allah.

Murmushi Halima tayi sannan tace, Kiyi Hakuri.

Aunty Suhailat, bantaba kasancewa cikin soyayya ba ballan tana nasan yadda lamuran cikinta suke.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now