*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖
'''🅿️ART 3️⃣'''
*PAGE 3️⃣*
'''THE NEXT DAY.
LATEEF OFFICE.
Salman ne zaune shida Lateef suna maganah.
Bazakaje gidansu Nadian Bane? Salman ya tambayi Lateef.
Kallansa Lateef yayi da cewa Salman mene amfanin zuwa na bacin wadda zanje wajenta bazata ganeni ba.?
Uhm Lamarin nan akwai rikitarwa sosai Lateef.
Amman abin nikuma yama fara tsoratani fa...
Domin ni duk wanda nasani da irin wannan lalurar idan har yaga wani daya taba sani a baya yakan iya ji kaman yayi rayuwa dashi.Amman ita Nadia tana rayuwa a cikin wadanda ta sani a baya amman bata iya gane koda mutum daya abin da mamaki fa.
Salman wannan shine typical Example na ikon Allah!
Allah idan yaso babu ta yadda baya iya juya lamarinsa.
Dondai ya bawa bawansa mamaki.
Nikaina ina yawan tinanin wannan Al'amarin Salman to Amman abinne duk rikitarwa tafi yawa a ciki.
Hakane gaskia!
To Allah ya bata lafia dai.
Wannan soyayya muga inda zataje...Salman kamar yaya muga inda soyayya zataje?
Hmm Lateef kenan shin ka mantane wai nace maka ni bazan kara goya maka baya akan soyayyar ka da Nadia ba.
Wai Salman dan Allah meyasa bakason a zauna lafia ne?
Ni wai mena maka ne haka tinda akayi case dinnan na wajen Abu Adam duk kabi ka canja.
Kafadamin idan kanada Alaqa da Abu Adam dinnan?
Hmmm Lateef aida inada Alaqa da Abu Adam da ba sai yanzu ne zaka sani ba.
Ba ina Magana ne akan Abu Adam ba.
Ina magana ne akan Sarah...
A koda yaushe kaine kake takuramin da Magana akan Sarah.
Bakada magana koda yaushe sai ta Sarah.
Bacchi, Wanka, Abinchi.
Komanka Sarah kake Ambata.
Lateef idanna zauna ina tinani sai naga duk yadda kakeson Nadia bai kai kwatan kwatan yadda kaso Sarah ba.
Shin a hakanne kakeso na yadda haryanzu baka sonta?
Lateef lokaci yayi da zanfito fili na fada maka abinda kai kake boyemin bakaso na sani.
Lateef shin meyasa Sarah Take kiranka A waya?
Meyasa Haryanzu Itace a Bio dinka na Social media.
Sunan tane?
Shin Bakada Ra'ayin canjawa ne kome?
Lateef dafe kansa yayi sannan yace A koda yaushe kaikuma bakada magana saita Sarah.
Kasani Sarah Tarihi nace.
Kuma Sarah tamkar watan Azumi ta ke a rayuwa ta.
Tashigo kuma ta wuce....
Bakayi karya ba tabbas naso Sarah Amman a baya kasani banda yanzu...
Sannan wannan tambayoyin naka banida Amsoshin su Salman.
Idan kamatsu da sanin amsoshinka saikaje ka nemo inkaga dama zaka izuwa ma ka tambayeta da kanka.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
Fiksi UmumLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?