*RAYUWA TA THE NOVEL📔📖*
'''PART FOUR 4️⃣'''
*🅿️AGE 7️⃣*
'''GIDAN ALHAJI ABDULLAHI.
Aslam bakada hankali ne?
Nadia fa kace?Daddy nayi tinanin zan iya mantawa da ita bayan duk tsawon wannan lokacin amman a koda yaushe idanna bude idona, koda bacchi nakeyi ko abinchi nake tinawa babu wadda take zuwa raina sai Nadia.
Daddy Ka auramin Nadia shine kadai gatan da zakamin a duniya ka gama dani.
Tashi Aslam yayi yace Nagode da duk dawainiyar ka a gareni sannan ya wuce izuwa dakinsa.
Kai?
Wai wai waishin yaushe yaron nan ya zama mara kunya hakane?Kodai ya fara shaye shaye ne dai bamu sani ba?
Alhaji duka ba wannan zaka kalla ba, Aslam lafian sa qalau,
Alhaji Aslam fa sunyi wata iriyar shakuwa ne shida Nadia bazaiyu dama ace zai daina sonta lokaci guda ba.
Alhaji nidai a ganina ka duba maganar sa, ayi masa abinda yakeso.
Wai kema biye masan zakiyi komene?
Ok! Yanzu naceda Ammie me? Fadamin.
Cewar Yanzu Aslam ya dawo kuma Nadia yakeson ya aura ?
Fadi mana Inajinki?Alhaji ba haka nake nufi ba Ina nufin Ita Ammie babu ruwanta a ciki.
Zata aurama Nadia wanda takeso ne kawai.
Nidai Alhaji kaji maganar Yaron nan dan Allah.
Tabbas da gasken Munsani cewar yana sonta.
Kada mujefa rayuwarsa a wani halin kuma.
Shiru Alhaji ABDULLAH yayi.
DA DADDARE.
Lateef ne shida Salman cikin Mota,
Nusaiba da Nadia ne suka fito.Shiga gaisawa sukayi da Lateef da Salman din.
Kayi kyau fa!
Hmm Da Gaske?
Da gaske Mana....
Ok! Yanzu shiga mota muje toh wannan daren dake zan batashi.
Nadia ce ta bude mota suka shiga itada Nusaiba.
Yanzu dai fatan bakuci komai ba don inaso muje mu farayin Dinner kuma zaku rakani shopping.
Idan kuma kunada abin saya toh?
Hmmm Mudai bamuda abin saya saidai mu rakakan kawai fadin Nadia.
Hmm dama ke nasan abinda zaki fadi kenan Nusaiba kefa aike nasan zaki sami abin siya ko kuwa.?
Hmmm Ai ta rigada ta fadi Amsar mu duka cikin wasa Nusaiba ta fadi.
Tafia sukeyi a Mota har suka isa wajen cin Abinchi.
GIDAN ALHAJI ABDULLAH.
Mahaifin Aslam ne ya shigo, Alhaji sannu da dawowa.
Yauwa sannunki dai yana ganki keke kadai ina Aslam din koya fita ne?
A ah, Aslam fa tin safe yau baima fita ko ina ba.
Yana dakinsa,
To meyafaru haka bai fita ba?
Bandai sani ba Amman bazai wuce maganar da kukayi dashi dazu ba.
Mahaifinsa girgida kansa yayi yace Inazuwa barina fito dashi.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
Ficción GeneralLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?