RAYUWA TA PRT 2 PAGE 2

9 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL✍🏽📔*

✨ _PART 2_ ✨

2️⃣

'''GIDAN ALHAJI RAUF.

Me Gadi ne zaune kan benchi yanajin radio.

Nadia ce ta sauka daga Napep, Sallama Tayi masa.

Me gadin ya Amsa mata da kuma tambayarta wajen wa tazo.

Dan Allah Wajen Abdul Lateef nazo ko yana nan inaso kamin magana dashi.

Ehh yana ciki bari ayi miki magana dashi koh.

Ciki me gadin ya nufa don sanar da Lateef din.

Babban Parlor yaje inda Lateef din yake zaune yana kallo.

Sanye da wata Jallabiya a jikinsa mai shegen kyau.

Hadi Yaya?

Dama Yallabai watace tazo wajen ka tace in maka magana.

Amman Hadi nace maka duk wanda yazo ai ace bana nan koh?

Meyasa kai bakajin magana ne wai.

Yi hakuri Yallabai naga ita macece ne shiyasa,

Shikenan jeka jeka jeka kawai Ganinan.....

Hadi mai gadi ne ya fito sannan yace gashinan zuwa na sanar dashi.

Thomm Nagode Nadia ta fadi da dan murmushi.

Lateef ne ya fito yana kallan gefe Nadia ya gani a tsaye,

Kallan ta kawai yayi baice komai ba.

Dan Allah Ka saurareni Abdul.
Wallahi banyi komai dan yaudarar kaba.

Wallahi Kaine kadai wanda nakeso dan Allah karka rabu dani a lokacinda nikuma na kamu da tsananin sonka.

Nan da nan Hawaye suka fara fitowa daga fuskar Nadia.

Muryarta ta koma ta masu kuka.

Mene haka Nadia Ya kike kuka kuma?

Ciro Handkerchief dinsa yayi ya bata tareda fadin.

Share hawayenki kidena kuka banason kuka.

Daga Ina kike?

Nadia ce masa tayi daga gida.

Shikenan bari na dauko mota na kaiki gida Saimuyi magana a hanya koh.

Lateef cikin gidan ya shiga inda yace Budemin Gate kai!

Motarsa sak irin wadda ake yayi sabuwa Dallll...

Mai Asalin Tsada.

Dauko key din yayi a cikin Parlour sannan yazo ya shiga motarsa.

Ya fito, Nadia ce tashiga.

Inda suka nufi izuwa gidansu.

Amm! Nadia Tabbass ina fushi dake, Kuma Naji babu dadi sosai.

Saboda Kincemin Mahaifinki zai bayar dake, Nayi miki uzurin bakisan cewar Ina Sonki ba.

Amman na fada miki daga baya,
Meya hadaki da Aslam, da Khaleed.

Banda Allah yasa Anfahimci abin cewar dukansu ne suke sonki.

Da kenan ta yaya za'a kalleki?

Nadia Ina Kaunarki da gaske Hakan yasa Naji kishinki a wannan lokacin kuma hakan yasa raina ya baci.

Dukda kasan cewar ina fushi dake hakan bayaja sonki ya ragu bane a zuciya ta.

Yana nan yadda yake saidai ma abinda ya karu.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now