*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖
'''PART FIVE (5)'''
*PAGE EIGHT (8)*
'''GIDAN SU SARAH.
Radeeyah ce kan Gado Ita kadai tana Charting da Lateef.
Sakon sane yashigo inda aka rubuta,
"Dan Allah kiyi hakuri Wallahi Inason Sarah Bazan iya cin Amanarta ba.
Aurenta nakeso nayi, Kokadan banada niyyar cin Amanarta."
Radeeyah ce takaranta tace wallahi saika soni a zuciyarta.
Rubuta masa ta karayi,
'Ni bance kaci Amanar Sarah Ba, Kuma Naga kai Namiji ne zaka iya auren Mata Har Hudu idan Kanada Ra'ayi Lateef, Dan Allah kakarbi soyayya Ta'
Immediately Ya dawo mata da Answer cewar
"Kiyi Hakuri Radeeyah Ke 'yar uwar Sarah ce, bazan iya soyayya dake ba kisani Ansa Mana Rana da ita Sannan yayi Offline "
Radeeyah murmushi tayi da fadin wallahi zaka shigo hannune Lateef indai nice.
Wallahi saika yarda kuma saika soni.
GIDAN ALHAJI ABDULLAH.
Ammie tace bataso na kara magana akai wannan shine dalilina na yin shiru.
Amman Alhaji Wannan Fa batan Mutum ne bawai batan wani abu karami ba.
'Yan sanda sunki kawo wani jawabi haryanzu.
Anqi ganin Aslam haryanzu bamu sani ba yana raye ko yana mace?
Kulll..... Karna karajin kin fadi haka, kinjiko.
Aslam yana raye babu abinda zai sameshi.
inshaAllah.
Ammie tana iya bakin kokarinta, Banaso na nuna mata Aslam ba danta bane.
Shiyasa na barta akan lamarin, Amman har cikin zuciya ta wallahi Hankali na a tashe yake.
Tashima ki daukomin Magani na do Allah.
Mahaifin Aslam yaceda Maman Aslam.
GIDAN SU NUSAIBA.
Umma inshaAllah A cikin satin nan,
Hmmm Badai don kinji mahaifinki na yawan matsa miki bane kikaje zaki turo wani don murabu dake.?
Bahaka bane Wallahi Umma, Wannan a Office dinmu yake.
Da nice nake masifar sonsa, tokuma Kafin na furta masa ma Allah ya karkato da tinaninsa izuwa kaina.
Yanzu sona yakeyi kamar yayi hauka.
Masha Allah, To Alhamdulillah! Ai gwarama da bakiyi gaggawa ba yanzu ya fada da bakinsa.
Kinga da bazai sokin nan kaman hauka ba tinda kece kika fara furta masa.
Hmm hakane Umma.
Ina Baban Yake?
Ehh Mahaifin ki dai yadan fita Amman duk inda yake zai dawo ai lokacin shigowarsa gidane yanzu.
Ok, Naganeh thomm zanjirashi tinda babu inda zanje.
Ya kuwa, labarin Aslam?
Uhmm, Umma ai labarin Aslam dai.... Tohh 'yan sanda dai sunata bincike.
Amman haryanzu basu kawo wani hujja ba da take nuna Ansameshi.
Amman sunadai kan binciken Haryanzu.
Allah sarki Ni Nadiar ma nake Tausayi wallahi Nusaiba.
Yarinya Da kuruciyarta, Da Naje idonta duk ya kunbura da kuka kana gani kasan tasha kuka.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
Ficción GeneralLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?