RAYUWA TA PRT 2 PAGE 3

14 2 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔

✨ _PART  2_ ✨

3️⃣

'''WASHE GARI.

GIDAN ALHAJI RAUF.

Lateef ne zaune shida Mahaifiyar sa suna Magana.

Kiran waya ne ya shigo masa.

Nadia ce akan Layi dagawa yayi Hello.

"Hello"

Barka dai Yakike Ya yau Nadia!

"Lafia lau Alhmdullh
Fatan Kaima Kana Lafia?"

Ina Lafia Nadia.

Zamzo Anjima kadan idanna Fito daga Gida zankaiki wani waje.

"Bana Gida yanzu haka ina Asibiti"

Asibiti kuma? Mekikajeyi a Asibiti?

"Wallahi Jikin Baba ne ya tashi tinjiya cikin dare shine muke Asibitin tinjiya dukan mu."

Subhanallahi!!! Amman Meyasa baki kirani ba Nadia?

"Dare ne Fa aikaga baikamata na kiraka ba tinda Darene Nakuma san ka kwanta."

Kinga wannan ba hujja Bace kuna wane Asibitin.?

Kashe waya Lateef yayi, mahaifiyar sace ta tambayeshi meyake faruwa?

Mama Wai mahaifin su Nadia ne bashida lafia kuma bata kirani ta sanar dani ba tin jiya wai na kwanta.

Kiji wata wauta fa...

Hmmm To ai Hankalin kenan Abdul Lateef.

Hakan shine dama ya kamata, sokake ta kiraka ta takura maka da daddare.

Gwara data bari saida Safe yanzu bagashi ba saikaje.

Mama Amman kuma da wani abu ya faru fa?

Kaga wannan fadan naka fa bakada hujjar yinsa Abdul.

Yarinya tayi daidai.
Wannan ai shine sanin ya kamatan.

Wannan yana daya daga cikin abinda yasa nake sonka da yarinyar saboda tanada Hankali.

Salman ne ya shigo cikin Parlourn bayan Yayi sallama.

Yauwa yanzu zankiraka dama.

Bama Hadi wannan Ya min dusting motana zamu fita yanzu.

Ina zuwa? Salman ya tambaya.

Mahaifin su Nadia ne aka kwantarshi Asibiti zamuje fadar Lateef yana hawa sama.

Bari nayi wanka.

Mama ce tacewa Salman wannan Abokin naka Kam sai a Hankali.

PRIVATE HOSPITAL.

Malam Amadu ne kwance kan gado.

Abu Adam yana zaune kan kujera, Nadia da Nusaiba suna Tsaye Sai Umma ma Akan Kujera.

Nadia Wannan ciwon Nawa dai nasan yazo karshe.

Domin yadda nakeji yanzu banajin zan kara kwana daya.

Haba Baba kadena fadin hakan,
inshaAllah zaka sami Lafia.

Bazaka tafi ka barni yanzu ba.

Nadia ne hawaye yake fitowa daga fuskarta.

Nadia Dan Allah kisamu kikula da Kanki, Kiyi kokarin kare mutuncinki.

Kada kisake kizubar da tarbiyar danake baki.
Akoda yaushe kyawawan halayenki sune karfin gwiwa ta.

Malam Ai Kana sata kusa, zaka tashi inshaAllah.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now