RAYUWA TA PART 6 PAGE 8

12 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL* 📔📖
          _( My Life )_

'''PART SIX'''

*PAGE  8️⃣*

'''Allah ya baki lafia Raheelah cewar mahaifinta,
Radeeyah tsaye take tana jiran zuwan Lateef.

Domin tasan cewar Rashin lafiar da Raheelah takeyi Saboda Lateef dinne.

Lateef dai baizo ba har su Raheelah sukabar kasar!!!

AN DAWO LABARI.

Lateef Girgida kansa yayi domin kokadan shi bai gane Radeeyah ba.

Mahaifin Sarah ne yace Shikenan ya isa, shine kika rikeshi saboda wannan kika taso tindaga kasar london don kawai kizo ki lalata masa aurensa?

To kinaji...

Wannan Abu ya rigadaga ya wuce.

Sannan saboda rashin abinyi shine zaki rike mutum a zuciyarki tsawon shekaru masu yawa?

Kuma kibiyoshi donneman daukarwa 'yar uwarki fansa?

Lateef shiru yayi baice komai ba, Sarah ma shiru tayi.

Radeeyah ba laifin Abdul bane kinaji, Mahaifin ku Sak yayi abinda nima nayi masa ne a baya.

Radeeyah Dan Adam bayason a wulakantashi.
Babu kyau yin hakan.

Tabbas idan koda Lateef yanada laifi to bai wuce nakin zuwa yaga halinda Raheelah take ciki ba.

Amman kiyi tinani Za'ayi miki irin abinda akayi masa kuma kije?

Bazakije ba Radeeyah, Saboda haka Lateef baiyi laifi ba.

Kuma Inaso Kijanye Sharrin da kikayi masa kuma kinemeshi yafiya.

A ah Abbah, Nine zanneme ta yafiya, Duk wanda zaizo musamman donyi maka haka a lokacin aurenka.

To tabbas shikadai yasan abinda yaji a baya.

Nasan kinsan Sonda nayima Raheelah na gaskia ne koda a baya.

Sam banda niyar cutar da ita, Amman kiyi hakuri Abisa Abinda ya faru da ita.

Radeeyah Kallan Lateef din tayi itama cikin yanayi na yafiya.

Allah Ya Yafe Mana Baki Daya Abinda ta fadi kenan.

Kutashi Kuje Mahaifin Sarah yaceda Radeeyah da Sarah din.

Aunty Nafi Ma tashi tayi don basu waje.

Ahh Abinda Nakeso da kai Abdul, Karka damu.
Nafahimceka, Kuma Irinka Mace ya kamata ta aura.

Hakan yana nufin Zaka karemin Saratou bazaka taba barin wani abu ya faru da itaba.

Inaso a koda yaushe kaci gaba da kasancewa kai kaji ko?

Thomm Abbah inshaAllah Zanyi kokarin hakan lateef ya fadi.

Yanzu kaje kuci gaba da shirye shirye don bazamu daga biki ba.

Lateef murmushi yayi da cewa Nagode Abbah Allah ya saka da Alkhairy.

Haba kaikuwa Karka damu ni ai banida matsala da kai.

Allah ya bada Sa'a kajiko..

Lateef yaji dadin yadda mahaifin Sarah ya fahimceshi sosai.

Tashi yayi sukayi sallama ya fito waje don Tafiya.

Motar sa ya bude Ya Shiga Sarah ce ta fito daga gidansu sannan ta tinkaroshi.

Zuwa tayi ta tsaya jikin motan sa, batace komai ba.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now