RAYUWA TA PART 5 PAGE 3

13 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''PART FIVE (5)'''

*PAGE THREE (3)*

'''Dama duk tsawon lokacin nan kaine kake turomin da wannan sakon?

Khaleed dago kansa yayi da fadin Meyasa kika auri wani ba niba?

Meyasa Aka hada baki dake aka yaudareni aka turani wani waje don kiyi aure?

Khaleed me kake fadane haka? Mekake nufi..

Nadia kinfi kowa sanin abinda nake nufi, Nasoki kamar Zanyi hauka.

Infact nama fara haukacewa, Amman aka Rarrasheni Daniyayyar nabar kasa naje na kula da kasuwancin mahaifina.

Inacen Naga Ana bikinki,
Babu wanda na fadawa zan dawo ko mahaifina baisan na shigo kasar nan ba duk saboda ke.

Nadia ina sonki kuma bazan daina sonki ba.

Nadia kizo muje muyi aure, fadar Khaleed.

Kayi haukane Kome Khaleed?

Dama na haukace ai Nadia kinrigada kin haukatani tin abaya.

Kaga Khaleed kayi hakuri yanzu ni matar aurece.

Kadauki kaddarar rasani kasami wata....

Wata????

Wata ce kikace? Nadia babu wata wadda ta kaiki, babu kuma wata wadda ta isa na sota inba keba.

Nadia wallahi tallahi idan bansameki ba zan mutu kuma ba nikadai ba.

Kowa zai rasaki..

Khaleed meyasa kake fadin haka,
Bazaiyu na aureka ba saboda inada aure.

Kasani Cewar Aslam Miji nane.

Nadia Yaudarata Akayi Kikayi aure wanda da ina wannan kasar hakan bazai taba yiwuwa ba.

Zanbaki nan da kwana biyu kiyi tinanin koma mene Amman nidai kizomin da maganar da zan fahimta.

Dama kina tambaya na na haukace ne, Idan bakizomin da Magana me Ma'ana ba Nadia lallai

Zaki sami Amsar ki Akan Lafia lau nake ko kuma na haukace din da gaske.

Khaleed juyawa yayi izuwa Motar sa ya shiga.

Nadia Tinani ya jefa ta, Domin kuwa A halin yanzu batasan kuma abinyi ba.

GIDAN SU SARAH.

Radeeyah ce Itada Sarah zaune cikin dakin Sarah.

Yanzu ke shikenan da bazaku zoba keda Raheela?

Hmm Saratou kenan, Nifa Saboda kema nazo kasar nan inba haka ba Mezanzo nayi.

Dangin mahaifin mu suna cen Aunty Nafi ce kadai dake kuke anan...

Raheela kuma Kinsanta, Bawani ishashshiyar lafia gareta ba.

Wai bataji sauki bane haryanzu?

Taji sauki mana kawai dai sometimes ne saikiga kaman bata hayyacinta.

Allah Sarki, Allah ya kara bata lafia dai cewar Sarah.

Ameen ameen,

Ke Amman kinyi Sa'ar miji Saratou.

Hmm Allah koh? Radeeya.

Ehmanah sosai ma daga ganinshi bashida matsala.

Hmmm Zangabatar mishi dake ai gobe idan yazo.

Tinda yau baku hadu ba.

Thomm Allah ya kaimu Fadar Radeeya.

GIDAN ASLAM

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now