RAYUWA TA PART 5 PAGE 12

7 1 1
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖

'''PART FIVE (5)'''

*PAGE TWELVE (12)*

'''GIDAN ALHAJI ABDULLAHI.

Nasani yadda kike cikin matukar damuwa, Bakuma kekadai ba.

Nima ina cikin matsananciyar damuwa dangane da Wannan Al'amari.

Banason Ammie taga kamar bata kokari akan wannan case hakan yasa nayi shiru.

Tacemin nabar mata komai a hannunta, Nasan cewar zatayi duk abinda ya kamata.

Cikin Yanayi Na damuwa Mahaifiyar Aslam tace Nasani Cewar Kobaka raye Ammie zatayi iya bakin kokarinta wajen ganin Aslam ya dawo.

Damuwa ta ba akan Rashin Ganinsa bane, Akan Halin da yake cikine yanzu.

Shin Yana Cikin Koshin Lafia?
Yaci Abinchi?

Shin Yana samun Ishashshen Bacci?

Duka wadannan Abubuwan sune nake tinawa suke dagamin hankali.

Alhaji Abdullahi gyara Zamansa yayi inda yace, Tabbass Wannan shine Babban Abinda Nima yake dagamin Hankali.

Duk da nasan cewar duk inda Aslam yake a halin yanzu hankalinsa yanakan Ahalin Sane duka.

Ki karfafa Zuciyarki inshaAllah Dan ki Zaidawo Gareki.

Yajikin Ita Nadia din?

Nadia Tana Tareda Ammie a koda yaushe, kuma tana cikin Koshin Lafia.

Allah Ubangiji Yasa Aslam ya dawo kafin Nadia ta haifi Dansa.
Cewar Mahaifiyar Aslam din.

inshaAllah Kuma In Allah ya yarda zai dawo Allah zai dawo Mana dashi.
Inji Abdullahi.

GIDAN SU NUSAIBA.

Dama Shine Mukace Bari Muzo don Nemama Yaro Auren Ita Ah 'yar ku din.

Waliyin Salman ne  yake magana da Waliyyin Nusaiba da kuma Mahaifinta.

Hakane, Ahh Babu damuwa, Ai Shi Aure Ibadane.

Kuma duk wanda yace yanason Naka, Toh Fa Babu abinda zaka biyashi dashi.

Nine Yayan Mahaifin Ita wannan Yarinya.

Kuma Munbashi aurenta Munyarda dashi A matsayin wanda zata aura in Allah Ya yarda.

Masha allah, Alhamdulillah.

Duk Abinda Ya Kamata ayi na biki inshaAllah Zanuyi iya bakin kokarin mu wajen ganin Anyishi.

NAN DAI MAGABATAN SALMAN DA NUSAIBA SUKAYI MAGANA.

INDA AKA BAMA SALMAN NUSAIBA A MATSAYIN WADDA ZAI AURA.

WANI WAJE A GARIN GWANAYE.

Yanzu Kallan Mahaukata fa suke Mana,

Khaleed ya kamata muyi wani abu akan wannan.

Wannan Shirun da mukeyi ya farayin yawa, Ya Kamata Ace Munyi wani abuda zai nuna musu cewar da gaske fa muke ba wasa muke ba.

Suhailat take fada.

Suhail Karki damu Inada Babban Target Akansu Duka.

Kuma Wallahi Tallahi Zasuga Tsantsar Hauka.

Suhail inason Nadia kuma wallahi Tallahi Idan ban sami Nadia ba.

Hankalin kowa bazai taba kwanciya ba.

Zaman lafian su kawai susan yadda zasuyi su auramin ita.

Khaleed Babu abinda bazanyi ba don samin Aslam a matsayin miji na.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now