RAYUWA TA PART 4 PAGE 4

9 1 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL📔📖*

'''PART FOUR 4️⃣'''

*🅿️AGE   4️⃣*

'''NADI'S OFFICE.

Zaune Nusaiba Take Kan kujera a Office din Nadia.

Nadian ma tana zaune.

Amman Nadia nidai bana ganin wannan Dabara ce, wannan kasada ce... cewar Nusaiba.

Nusaiba banida wani zabi fa, Indai Har Lateef zai fito nishine kawai abinda nakeso.

Amman Nadia da kinbi komai a hankali kefa yanzu zakiyi hakanne donshi.

Amman idanya fito ya kuma gano cewar gata yadda ya fito kisani ba lallai ya fahimceki ba.....

Sannan duk wannan Abin da kikeyi baki sanarwa da Ammie ba?

Nusaiba hakane, Ba lallai ya fahimceni ba.

Amman duka Nayi ne don sonsa da nakeyi.

Hakane Nasani Nadia nasani,

Amman kema ya kamata kisani koda ke ko babu ke Ahalin Lateef bazasu taba barin sa cikin wannan halin ba.

Kinfi kowa Sanin Hakan.....

Knocking Kofar  Office din akeyi Nadia tace Shigo,

Rankishi dade Oga Mukhtar ne keson Ganinki Yana Office dinsa cewar Masinja.

Ok! Kace Ina Zuwa.

Bari Na dawo sai Muje Wajen Ammie Koh? Fadar Nadia kafin ta fita daga Office din.

GIDAN ALHAJI RAUF.

Elham ce take waya da mahaifinta tana zaune a parlour.

Ok! Daddy babu damuwa Zan sanar da ita inshaAllah.

Katse Wayar tayi bayan Mahaifiyar ta tazo Parlourn ta zauna.

Mummy Daddy yace Dama Ya Abdul ne yakeson Ganinki ko hankalin ki zai kwanta.

Amman Ance ba'a barin kowa ya ganshi Ai?

Ehh Mummy amman ba in Hajia Ammie tana nan ba.

Yace Mushirya zaizo zamuje dukan mu harda Ammie ma.

Shikenan babu Damuwa.

Kitashi ki shirya din, Kafin yazo.

MUKHTAR'S OFFICE.

Nadia meyake damun kine?
Kwana Biyu aikinki ya sauya ba kamar daba?

Na duba Office dinki dazu naga Files din mutanen nan haryanzu ko budeshi bakiyi ba...

Nadia meyake faruwa dakene?

Oga Mukhtar Ni Kaina nakasa gane meyake faruwa dani,

Abinda kawai nasani shine Hankalina ba'a kwance yake ba.

Indai har Lateef bai fito ba.

Gyara zamansa Mukhtar din yayi da fadin kinga Nadia Lateef zai fito.

Nan bada dadewa ba Ammie tacemin cikin wannan Satin Zai fito.

Kidena Damuwa Kinjiko, Amm!!!

Abinda za'ayi Ina Ganin Ya kamata Kisamu hutu.

Kisamu ki huta Idan Allah yasa ya fito hankalinki ya kwanta saiki dawo bakin aiki koh?

Nadia cewa tayi Idan Ina zuwa Office Inadan Samin sauki.

Banajin Zama a gida zaisa naji dama dama.

Karka damu Oga Mukhtar,

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now