RAYUWA TA PRT 1 PAGE 4

27 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL✍🏽📔*

_Page 4_

'''PRIVATE HOSPITAL.

Ok! Doctor inshaAllah zamu kula sosai, shine rashin Lafian a jikinsa yake amman baya kulawa.

Nice zance masa lokacin shan Magani yayi, Mahaifiyar Khaleed ce a office din Doctor.

Suhailat da Khaleed a zaune.

Malam Khaleed saikana kulawa sosai pa Allah ya kara maka Sauqi fadar Doctor.

Thomm Doctor Nagode Sosai zankula inji Khaleed.

Tashi Sukayi Inda Khaleed ya mikama Doctor hannu yace Nagode.

Thom Malam Khaleed Allah ya kara sauki.
Ameen Doctor.

Fitowa Sukayi daga Office din Doctor bayan Sunyi Sallama.

Tsaye Khaleed yake shida Suhailat Giftawar Nadia Khaleed ya gani.

Zuwa tayi itada Nusaiba suka wuce suna Magana.

Khaleed kam bin Nadia kawai yayi da kallo.
Muje Mama ta fita!!! Abinda Suhailat take cewa kenan.

Amman Hankalin Khaleed baya jikinsa ballan tana yaji metake cewa.

Yarinyar dayabi da kallo Itama ita take kallah,
Khaleed!!! Suhailat ta kira sunansa ta tabashi.

Na'am Na'am Suhail, Mekake kallo ne haka? Inata magana hankalinka yayi wani wajen.

Suhail, Ina kallan Halittar Allah ne,
Tooh! Pa ikon Allah yaukuma kaine kake yabon wata,

Murmushi Khaleed yayi sannan yace dama banga wadda zan yaba bane sai yanzu!

Suhailat Yarinyar cen tayimin Gaskia,

Khaleed daga ganin mace bakasan kowace ba kace tayi maka Haba mana?

Idan kuma matar aurece pa?

Kinga kada kisagarmin da gwiwa Mana, Yanayinta ya nuna ba matar aure bace.

Dana kalleta ba iya fuskarta na kalla ba, Naga Mayafinta a kafada yake

Matar aure kuma idan zatasa mayafi har kanta take rufewa.

Saboda haka ba matar aure bace.

Ohhh! Wai duk wannan kallon ne yasa ka gano hakan amman Khaleed kaima.

Kinga Nidai yanzu wannan yarinyar tayimin.
Muje kirakani.

Hmmm Khaleed kenan Muje in raka ka fa kace?

Ehmanah kinsani bantaba samun kaina a irin wannan yanayin ba, bansan tayaya zanje mata ba.

Kingama suntsaya jikin wata mota subiyu abinsu.

Ehh Hakane Kam idan ban raka Abokina ba wazan raka muje toh.

Amman Mama tana mota fa?

Manta da Mama Muje Suhail fadar Khaleed.

___Kinga Kefa yanzu daidai kikayi, koda Abu Adam yadawo bakida laifi.

Mene abin Fada daga taimako, kuma naga Lateef shine ya kawo kansa ba zuwa kikayi kikace lallai saiya taimaka muku ba.

Banda madai abu irinna Abu Adam yaya daga taimako abu kuma yazama Fada.

Nusaiba ce take fadin haka.
Assalamu Alaikum..

Khaleed da Suhailat ne sukayi Sallama.

Amsa musu Nadia Tayi itada Nusaiba,

Kawata wajenki Nazo Suhailat tafadama Nadia Haka.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now