*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖
'''🅿️ART 3️⃣'''
*PAGE 8️⃣*
'''GIDAN ALHAJI RAUF.
Mota Akayi Parking Sarah ce ta fito daga cikin motar tata.
A kofar gidan su Lateef.
Hadi me gadi ne yace sannu da zuwa rankishi dade.
Yauwa sannunka Hadi fadin Sarah.
Dukda fuskar ta dai Alamun babu dadi.
Shiga tayi har cikin Parlourn gidan Bayan tayi Sallama.
Lateef ne zaune kan kujera yana kallan TV.
Kallan ta kawai yayi sannan ta zauna.
Ina yini Sarah ta gaisheshi,
Amsa mata yayi da cewa Lafia lau.Ya su Mama?
Duka suna Lafia sunfita ma bakowa a gidan nima ina hutawa ne kafinna fita kuma.
Dan Allah kayi hakuri Lateef!
Lateef kallan Sarah yayi,
Hmm .Wallahi naji babu dadi matuka Abinda Abbah yayi maka.
Kuma nima na nuna masa banji dadi ba Dan Allah ina baka Hakuri a madadin sa.
Sarah mahaifinki baiyi laifin komai ba.
Sai yanzune na gane cewar abinda nayi a baya tabbas zai bibiyeni.
Gashi kuma.
Sarah nine wanda ya kamata na bawa mahaifinki hakuri akan abinda nayi masa a baya.
Sarah wannan ba wani abu bane Kuma na cancanchi fiye da haka a wajen mahaifinki.
Wallahi ni kunyar hada idoma nayi dashi.
Dan Allah ki kara bashi hakuri.
Kuma zan kara zuwa na bashi hakuri Da kaina koda zai dauki matakin dayafi wannan ma a kaina.
Cikin wani yanayi na shauki Sarah ta kalli Lateef din tace INA SONKA!!!
dagowa yayi cikin Mamaki da tambayar me kikace?
Ehh kwarai ina kaunar ka Lateef.
Na fada maka dama zan kara furta maka kalmar so ne idan har ka gane kayiwa Abbah ba daidai ba kuma kake kokarin bashi hakauri idanka manta niban manta ba.
Dukda kasancewar kayi fushi kace indai hakane to munrabu da kai kenan.
Nasani cewar wata rana dole Saikasan kayi ba daidai ba kuma saika bada hakuri.
Domin nasan halinka fiye da kowa Lateef.
Saboda Rashin jurar rasaka ne yasa na bar wannan kasar dukda kasan cewar Abbah yaso hadani aure da mutane da yawa naki amincewa.
Da yasan cewar kaine dalili na nakinyin aure da ko auren dolene saiya yimin Lateef.
Amman Ni kaine dalilina na kinyin aure haryanzu.
Kuma a jikina nakejin tabbas kamar yadda muka rayu a baya yanzuma zamu rayu domin Har yanzu kana sona.
Salman ne ya shigo cikin gidan Bayan yi masa sallama.
Kada ka bata Amsa cikin gaggawa kaji.
Lateef ne yace Kasan meta fadi ne Salman?
Kwarai Lateef nasan me tace, domin bata fada maka ba saida tayi shawara ma dani.
Mekake nufi Salman?
Hmmm. Lateef lambar Sarah da take cikin wayarka Wanda na titsiyeka nine wanda ya saka maka ita a cikin wayar ka.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?