*RAYAUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔
✨ _PART 2_ ✨
1️⃣2️⃣
'''DA DADDARE.
GIDAN ALHAJI BASHIR.
Suhailat ce Zaune a Parlourn Mahaifinta sai Momyn ta.
Alhaji bashir ne yace, Thom dama Ba komai bane yasa nace inason magana daku duka illah na sanar daku wani muhimman sako.
Ehmm Suhailat yau kamar yadda nayi Alqawarin zan kira Aslam tona kirashi.
Yazo har Guest house dina munyi Magana dashi Suhailat abinda nakeso dake shine.
Kimanta da Aslam bazaki aureshi ba!!!
Cikin wani Hali ta dago ta kalli mahaifinta,
Hada ido sukayi da Mommy.Daddy kaji mekace kuwa?
Kwarai Suhailat naji menace.Zankuma Maimaita miki, Kimanta da Aslam domin bazan bari ki aureshi ba.
Basa'an aurenki bane!
Amman Alhaji meyafaru ne haka?
Kallan ta yayi yace Banasonki a maganar nan fateemah.
Kibarni da Suhailat nake Magana.
Nakiraki ne kawai donki zama shaidah.Kuka Suhailat takeyi inda Tace Daddy menayi maka?
Dan Allah Daddy katausayamin.Tashi Yayi inda yace Saida Safe.
Mommy ce tadawo inda Suhailat take ta ce kidena kuka.
Mahaifinki bazai yanke wannan hukuncin kai tsaye ba dole akwai abinda ya gano.
Zanyi magana dashi zanji dalilin yin hakan.
Kinjiko kije ki kwanta yanzu cewar Mommy.
Suhailat kam dai haka ta tashi izuwa sama dakinta.
Kwanciya tayi tana kuka, Ko Kayan barcinta data saba sawa bata saka ba.
Haka ta kwanta har bacci ya dauketa.
WASHE GARI.
GIDAN ALHAJI ABDULLAH.
Nadia ce jikin Mota, Itada Mahaifin Aslam da Maman Sa.
Aslam ne ya fito, Mahaifin sane yace haba Malam sai jiranka mukeyi.
Nadia Kushiga keda Mama motar Aslam ni zantawo a wannan.
Nadia cewa tayi thomm Daddy,
Mahaifiyar Aslam ce itada Nadia suka shiga motar Aslam din.Kishiga Gaban Nadia cewar Mama.
Nadia Murmushi kawai tayi tace thomm Mama.
Alhaji ne Ya shiga Motar sa shida Driver dinsa.
Motoci uku sukayi inda suka dauki hanya izuwa Maida Nadia gida.
Aslam ne suke tafia, Shiru yayi baya cewa komai.
Ya kayi shiru? Nasan kana tinani ne akaina.
Nasan kuma zakayi kewana sosai.Fadar Nadia.
Aslam Kallan ta yayi, yayi murmushi da cewa Hakane!
Nadia ba Aslam kadai ba kowa a cikinmu zaiyi kewarki ba kadan ba.
Sannan wannan tafiyar da zakiyi itace zata kara mana kusanchi na har Abadah.
Nadia cewa tayi Mama Zanyi Kewarku fiye da yadda zakuyi nawa.
Mama Ba tafiya na nane banaso ba, Amman Mama kada Aslam yayi aure ya auri wata bani ba.
Hmm Nadia kenan, Mahaifinsa ya tabbatar masa da cewar lallai kece wadda zai aura.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?