RAYUWA TA PRT 1 PAGE 3

31 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL*✍🏽📔

_Page 3_

'''PRIVATE HOSPITAL.

Wata dalleliyar Mota ce tashigo izuwa Asibitin,

Ashh, Daga Gani tanada Matukar Tsada Motar kuma wanda sukeda kudine sukeda ita.

Wajen Parking akaje Inda akayi parking dinta.

Lateef ne ya fito daga ciki shida Salman,
Inda suke tawowa izuwa cikin Dakin da Mahaifin Nadia yake.

Direct Lateef Office din Likitan ya shiga shida Salman Abokin sa.

Sallama yayi sannan suka gaisa da likitan.

Abdul Kadawo kenan?
Ehh Doctor Na dawo wallahi zanma fitane nace barina shigo naga Jikin nasa saina wuce

Fadar Lateef.

Ok! Ehh hakanma yayi, Ai jikinsa yayi sauqi don yauma ina tinanin zan sallamesu sutafi inshaAllah.

Masha Allah, Babu wata matsala kuma Doctor?

Ehh Abdul babu indai sunbi duk wata ka'ida dana dorasu akai babu damuwa inshaAllah Cewar Likitan.

Thoo, maganar kudi fa?

Wannan sai za'a tafi tukuna shine zakayi clearance gaba daya ba yanzu ba.

A ah ai gwara nayi komai yanzu saboda bansani ba ko zandawo nan kusa kafin sutafi.

Karmuyi sabani amman idanna gama kaga banida wata fargabar wani abu daban Inji Lateef.

Ehh hakane to abinda za'ayi zanhadaka da Nurse kuje wajen Cashier din inyaso saiku gama koya?

Yeah! Hakan yayi yanzu bari naje na duba jikinnasa Lateef ya fada.

Abdul tashi yayi shida Salman, inda Suka Fito suka nufi dakin Mahaifin Nadia.

Nadia ce zaune itada Nusaiba sunrasa me yake musu dadi domin ga abinda Abu Adam yace.

Kuma basu fadama Umma ba domin sunsan ma Hankalinta bazai dauki shirmen ba.

Sunyi jigum Inda Umma tana Kan kujerar Roba ta zama kusa da Mal. Ahmadu.

Sallama Lateef yayi Shida Salman din, sannan suka shigo cikin dakin.

Daga shigowar Lateef din Wani kamshi ne ya mamaye dakin gaba daya.

Kamshin turare na maza mai karfi mai kamshin gaske kuma.

Mal. Ahmadu ne ya dan yunkuro inda Lateef yace A a Baba karka tashi.

Ke kutashi kubasu waje mana, fadar Mahaifin Nadia.

Nadia itada Nusaiba ne suka Tashi Suka fita daga dakin gaba daya domin kar ayi yawa.

Har kasa Lateef ya durkusa,
Ina wuni Umma?
Lafia Lau,
Yanayin gaisuwa Salman yanayi haka suka gaisa.

Baba Ya karfin jikin kuma?
Da sauki Abdul
Masha Allah, Allah ya kara sauqi.

Baba ya jikin kuma? Fadar Salman.
Da sauki Saurayi.
Allah ya kara sauqi Yasa kaffara ne
Ameen ameen.

Ai yanzu daga Office din Doctor nake Yace jiki yayi babu wata matsala yanzu.

Yamace Zuwa anjima kadan zai sallamemu.

Tohh! Masha Allah,
Mungode Sosai Mal. Abdul

Mahaifin Nadia yace,
Haba Baba ai babu komai wannan ba wani abu bane.

Sannan na gama duk wasu kashe kashen kudi, Babu wani abu da za'a kara biya kuma.

Toh ikon Allah Mal. Abdul ai Hidimar sai tayi yawa kuma.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now