*RAYUWA TA THE NOVEL*📔📖
'''PART FIVE (5)'''
*PAGE THIRTEEN (13)*
'''BAYAN AWA ASHIRIN DA HUDU.
PRIVATE HOSPITAL.
Kuyi Hakuri Hajia, Ansami Rashin Fahimta ne.
Domin Da suka dubashi suka sanar dani kawai na sanar dake.
Sai Bayan Munzo Asibiti Sukace Mana Suma Yayi ba Mutuwa Ba.
Dpo ne shida Hajia Ammie yake Mata Bayani.
Kowa na Ahalin Hajia Ammie yana Asibitin.
Babu damuwa Na fuskanceka,
Yanzu Ya akayi shin Angano wanda sukayi masa haka?Kamar yadda na sanar dake a baya shine Murtala Mora shine babban wanda muke zargi.
Kuma Munsami Nasarar Kama Daya daga cikin Yaransa.
Munyi Amfani da shine inda yayi leading dinmu garesu.
Amman bamu sami masarar kamasu ba duka.
Suntsere bayan sunsami labarin 'yan sanda suna nemansu.
Murtala Mora Ya Bada Umarnin Su kashe Aslam su jefar dashi.
Sunyi Masa Allurori sosai wanda shiyasa haryanzu baisan inda kansa yake ba.
Sannan suka jefar dashi.
Amman Alhamdulillah Munkama Biyu daga Cikinsu amman bandashi Murtala Mora din ya gudu.
Ammie sauke Numfashinta tayi, Abdullahi wato mahaifin Aslam ne yace.
Duk yadda za'ayi akamashi a kamashi Dpo domin bazan taba yafe masa ba akan abinda yayima Dana.
Karka damu, inshaAllah Shima zai shigo Hannunmu kuma zai fuskanchi hukunchi daidai da Abinda ya aikata.
Dpo ya fadi, yanzu zanje zamu cigaba da bincikar Wadancen da suke hannu.
inshaAllah Duk abinda yake da akwai zan sanar daku.
Shikenan Dpo Mungode Kwarai Fadin Abdullahi.
Doctor ne ya fito daga inda Aslam din yake.
Doctor yaya yake? Mahaifiyar Aslam din ta Tambaya cikin hawaye.
Nadia Ma Tashi tayi duk bata hankalinta Tayi Jajawur don kuka.
Amm Da Alhaji Inason Ganinku a Office dina Saimuyi Maganah cewar Doctor.
Abdullahi, Mumin Da RAUF ne sai Ammie suka Bi Doctor izuwa Office dinsa.
Doctor meyake faruwa ka sanar damu Mana Ammie ta fadi.
Zauna Hajia Ku zauna Dan Allah Inji Likita.
Zama sukayi,
Ahhh Hajia Aslam Yana Raye Bai Mutu ba ku kwantar da hankalin ku.
Sunyi Amfani da Allurar da akeyima Mata idan sunzo haihuwa.
Sunyi Masa ita a jikinsa wanda harta fara Bata Masa jininsa.
Yakai Kusan Kwana Uku Zuwa Hudu baya cikin hayyacinsa.
Domin sunsa Allurar tazama masa jiki Sunsa ta bugar dashi.
Ahalin da Ake ciki yanzu dai Ana bukatar Ayi gaggawar fita dashi kasar waje.
Domin Yi masa Zubbi Ma'ana Canjin Jini.
Bawai Bamayi Anan Ba.
Amman Kayan Aikin Zasufi karfi nacen.
YOU ARE READING
RAYUWA TA THE NOVEL
General FictionLABARIN 'YAN UWA GUDA UKU DA KOWANNE MAHAIFINSA KEDA DUKIYA, SUKAN SAMI DUK ABINDA SUKESO NAJIN DADIN RAYUWA SAIDAI KASH SUN HADU KAN SOYAYYAR WATA YARINYA GUDA DAYA SHIN YAYA ABIN ZAI KAYA?