RAYUWA TA PART 4 PAGE 12

8 0 0
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL📔📖*

'''PART FOUR 4️⃣'''

*🅿️AGE   1️⃣2️⃣*

'''DA DADDARE.

PRIVATE HOSPITAL.

Mustapha ne ya budema Hajia Ammie Kofar Mota ta fito.

Lateef ya rigada yayi mata kwatancen dakin Amenity 2.

Kaji rani yanzu zan fito ba dadewa zanyi ba.

Zara'u ce ta fito, Ke kuma muje kirakani.

Itada Zara'u ne suka shiga cikin Asibitin.

Alhaji ne shida Aunty Nafi tsaye ba'ace dasu komai ba dangane da Sarah.

Ammie ce ta gano su Alhaji, Alhajin Ammie ya gano tana tawowa.

Juyar da fuskarsa yayi, Karasowa tayi har inda suke.

Aunty Nafi ce ta gaisheda Ammie, Alhaji Kallan Ammie kawai yayi baice da ita komai ba.

Kaga Ka ajiye komai a gefe kajiko, Banazo nan ne don komai ba saidan kai kawai.

Ya kamata Ace ka sauya tinaninka da kuma gabar daka dauka Akai na.

Alhaji baice komai ba.

Ammie ce tacewa Aunty Nafi ya mai jikin?

Da sauki Ammie sunshiga da ita ciki tin dazu basuce damu komai ba.

Allah ubangiji ya bata Lafia, zataji sauki inshaAllah kinjiko?

Lokaci yayi da ya kamata ace kasan cewar rayuwa kullun gaba akeyi ba tsayawa ba.

Sarah yarinya ce mai hankali ilimi da tinani, Tanayi maka biyayya iya iyawar ta.

Amman meyasa kai bazaka iya biya mata bukatun taba?

Don tana soyayya da dan wajenane?

Kanaji Wannan ba daidai bane kasani kana cutar da 'yar kane.

Kuma kanayi mata wani tabo ne a jikinta idan baka sani ba.

Lateef yayi kuskure nayi maka rashin kunya, kasani ba goyon bayansa nayi ba.

Hasalima ina daya daga cikin wa'yanda suka bata masa akan abinda yayi maka dukda kasancewar koma meya fadi.

Kaine sila, Kasani Babu dan da zai haifu azagi iyayen sa a gaban sa yaki tankawa.

Ballan tana Ahalinsa baki daya,
Ba nazo nan bane don nasanar dakai wannan duka.

Nazo nan ne donna tsaida magana daya tsakaninmu da kai akan rashin lafiar 'yar ka.

Nasani kasani Kowa ya sani cewar sarah akan Lateef ne take kwance batasan inda kanta yake ba.

Shin zaka bari Jida kanka ya kashe 'yar kane ko kuma zaka bata abinda takeso?

Kwangilar da silar tane taja duk wannan abin bayan shekara daya kasa meta.

Nasan bakasan cewar nice na dawo maka da itaba ko?

Alhaji kallan Ammie yayi baice da ita komai ba.

Kasauya tinani akan Rayuwar 'yar ka idanka sauya Koda yaushe zamu iyayin magana akan rayuwar su baki daya.

Ammie cewa Aunty Sa'a tayi Allah ya kara mata Lafia saida safe...

Juyawa tayi ta tafi Zara'u tana jiranta a cen gefe.

Alhaji baice komai ba.

Doctor ne ya fito daga inda Sarah take, Alhaji da'Allah inason Ganinku mana.

Alhaji cewa yayi Ok thom Muje Doctor,

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now