RAYUWA TA PRT 2 PAGE 7

6 1 6
                                    

*RAYUWA TA THE NOVEL✍🏽📔*

✨ _PART  2_ ✨

7️⃣

'''GIDAN ALHAJI ABDULLAHI.

Kaga Nibarina tashi na wuce idan Mama ta tashi kawai kagaisheta.

Suhailat ce ta fadi haka.

Thom thom babu damuwa zataji zan sanar da ita.

Cikin murmushi inji Aslam.

Suhailat daukan jakarta tayi inda fita.

Aslam ne yay sauri ya tura kofar,
Kitchen yashigo wajen Nadia.

Nadia ce take kuka,

A ahh Nadia meyafaru kuma kike kuka me akayi miki?

Goge mata Hawaye zaiyi Inda tace Ni karka tabani.

Meyafaru Nadia kifadamin Mana Hankali na ya tashj Fa.

Babu wani Hankalinka daya tashi wannan ba gaskia bane.

Kafurtamin kalmar kana sona kuma zaka zauna tare dani bazaka barni ba.

Amman yanzu da kunnena naji kayima wata Alqawarin Auren ta.

Kafadamin shin saboda Ba'asan inda Ahalina suke ba shine yasa bazaka aureni ba.

Shin Laifi nane kasancewa na haka?

Nadia Ki saurareni Dan Allah!

Ba haka bane abinda kike tinani.

Sam kokadan ba yadda kike tinani bane,

Toyane idan ba haka bane?
Ba fadamin Akayi ba Da kunnena Najia Fa.

Babu Maganar Karyatawa...

Nadia Naji na fadi Haka kuma nima bankaryata Hakan ba.

Amman ba gaskia bane.

Nikawai karabu dani cikin fushi Nadia tabar Aslam cikin Kitchen a tsaye.

Girgida Kansa yayi da cewar Innalillahi Wa'inna ilaihi raji'un!!!

Ni meyake Faruwa da Rayuwa Ta ne?..

POLICE STATION.

Amman Abdul An tabbatar da cewar zai aikata hakan?

Dpo ne zaune shida Abdul Lateef a Office dinsa suna Magana.

Dpo, An tabbatar da cewa zai aikata hakan.

Domin koda tananan Babu irin shige da ficen da Bayyi ba wajen ganin ya rabata da kowa.

Anan bance shine ya dauketa ba saboda Bangani ba..

Amman Kuma Ina fadin abinda kowa yasan zai aikata.

Ok! Shikenan babu damuwa Abdul mene sunansa Kace?

Sunansa Abu Adam..

Kuma kace tinda ya tafi Kusan 4month kenan bai kara komawa gidan ba koh?

Ehh sunsanar dani  cewar tinda Nadia ta furta bata sonshi ya fita cikin fushi.

Yau kimanin watanni hudu kenan baikara jiyowa garesu ba.

Sannan wani Abin babban zargin shine Ranar da Ya tafi Ranar Sukayi wannan Accident din kuma shine ba'aga Nadia ba.

Dpo ba ina cewa shine sanadiyar Accident dinsu ba kokuma shirin sane.

Kamar yadda kowa yake zargi nima haka nake zargi.

Shikenan Na fahimceka Abdul,
Nakuma Gane mekake nufi.

Dpo, Dan Allah kuyi kokari wajen dawomin da Nadia.

RAYUWA TA THE NOVELWhere stories live. Discover now