MAHWISH PAGE 2

250 12 0
                                    


Har suka je suka dawo kuwa bata yi sallar ba, Hajiya ta yi maganar har ta gaji, babban abinda ya fi wa Mahwish mahimmanci shi ne Abban ta ya dawo ta ji a ina aka kwana.

Shiru, shiru, bai dawo ba, har sai da aka yi isha'i kamar yanda ya saba, ya na shiga ta fita da saurin ta dan ci gaba da tattauna maganar da take ganin ita ce mafita a soyayyar ta da Salim.

Gani ta yi bata ga Salim ba, kuma Abban ta ya rufe gida, tsaye ma yake a tsakar gidan ya na addu'a, (bayan an rufe qofar gida ana karanta ayatul kursiyyu a qofar gidan)da dukkan alamu ya gama fitar yau kenan, wani irin abu mai zafi da d'aci ta ji ya tokare mata wuya.

Wai me mutanen nan suke nufi kenan? Abban nata ma an juyar masa da kai kenan yanzu ba ya goyon bayan ta akan abinda take so? Inaaa dole ne yau Abban ta ya bata amsar abinda ke zuciyar shi game da maganar auren nan, cike da shagwaba da son yin kuka ta ce,

"Abbaaaa ina Salim? Ya na gan ka kai d'aya, Abbaa na zaci ka na baya na ne ashe kai ma ba ka son farin ciki na, Abbaa Salim nake so ni ba na son kowa bayan shi, ba zan auri kowa ba, Abbaa in kuka aura min wani ba Salim ba zan iya rasa rai na,"

Kukan da take danne wa ne ya kwace mata, ai kuwa ta sake shi, ta dinga rera shi kamar wani karatu, Alhaji Farouq kallon ta ya yi cikin tausaya wa, domin kuwa ya san yanda yaran ke son junan su, tun su na qanana, bacci ma ba ya raba su, sai dole, in yau wannan ya kwana a gidan su wannan, gobe wannan zai kwana gidan su wannan, sai da suka fara girma ne aka raba tsakanin su.

Dafa kafad'ar Mahwish Alhaji ya yi, ya ce,

"Mahwish dear, please stop crying, ya isa haka, tun dazu ki ke kuka, ba kya tsoron ciwon kai?"

"Abbaa ban damu da duk wani abu da zai same ni ba, rayuwa ta ba ta da wani amfani ko ma'ana in babu Salim a cikin ta, Abbaa ta yaya zan iya rayuwa da wani ba Salim ba?"

Da kyar Alhaji Farouq ya ja ta suka nufi parlour'n su, ya zaunar da ita, sannan ya kama hannayen ta biyu, ya na kallon kyakkyawar fuskar ta, da ke tsananin zubar da hawaye, ya na jin zafin kukan da take, amma ba shi da yanda zai ya sama mata mafita, ita suka haifa ba ita ta haife su ba, dan haka dole ne ta yi hakuri,ta bi umarnin su.

"Mahwish dear,tunda ki ke da mu a duniya kin taba neman wani abu kin rasa? (Kan ta ta girgiza alamar ahh ahh) wani abun ma Mahwish ba ku san da shi ba za mu yi maku shi, Mahwish ki na zaton ni mahaifin ki da yayu na za mu cutar da ke ? (Sake girgiza kai ta yi alamar ahh ahh) to me zai sa ba za ki iya yi mana biyayya ba akan wannan auren? Tunda kin san ba zamu cutar da ke ba, kuma kin san Sa'eed mutumin kirki ne, ko so ki ke na yi fad'a da 'yan uwa na musamman baffan ku? Ki na jin kalaman shi fa, ya ce dole sai kin auri Sa'eed in dai ba iyaka zan masa da iyali na ba, in nuna masa ni ma na haifa, ki na jin me Goggon ku Xulaihah mahaifiyar Salim din kan ta ta fad'a, ba za ta bari Salim ya aure ki ba, saboda in cancanta ake nema Sa'eed ya fi Salim cancantar ya aure ki, Mahwish 'yan uwa na ba da wani mugun nufi suke so ki auri Sa'eed ba, cancantar shi ce ta sanya aka zabe shi sama da d'an uwan ki na jini, Mahwish kamar yanda Baffan ku ya ce ne, marigayi mahaifin Sa'eed mutumin kirki ne,  kuma Sa'eed ya yo halayen shi na kwarai, ke yanda Baffan ku da mahaifin shi suka taso ai ko da a wani waje Sa'eed ya ke neman aure za mu tsaya masa har ya samu, ballantana ya na neman 'yar mu.

Mahwish na san tsoron ki ba zai wuce akan matar shi ba, matar Sa'eed kuwa ba ita ce abar dubawar mu ba tunda kowa da gidan ta za ta zauna, ba gida d'aya bane, idan ba ya gidan ki za ki sa a ran ki kamar ya yi tafiya ne, in kuma ya dawo wajen ki shike nan, mahaifiyar shi na tare da matar shi ba a gidan ki za ta zauna ba, na tabbata Sa'eed duk ya maki wannan bayanin.

Mahwish kar ki ce ban maki qoqarin a baki wanda ki ke so ba, na buga, na raya, kowa ya juyan baya akan wannan maganar,na rasa wanda zai duba lamarin ku ke da salim a gane ku na son junan ku fiye da tunanin kowa, amma duk yanda magana ta kai ta kawo, Sa'eed kowa ke zab'ar maki, dan Allah ki yi hakuri ki fidda Abban ki kunya, in isa da ke ko sau d'aya ne, kar ki watsan qasa a ido, a zarge ni da rashin baku tarbiyyar da za ku min biyayya"

MAHWISHWhere stories live. Discover now