MAHWISH PAGE 25

33 2 0
                                    

*Masoya karatun novels d'ina,ina miqo godiya da fatan alkhairi a gare ku, Allah ya qara mana son juna domin shi*

*Ina fatan za ku min hakuri saboda za ku dinga ji na shiru, ba za ku na samun post akai akai ba kamar yanda na saba a baya, saboda wani uzuri da ya taso min, amma inshaa Allahu, a duk sanda na samu sarari, zan yi maku typing kuma na yi posting ko da page nawa na samu damar yi kuwa, ina roqon addu'ar ku akan samun nasara akan abinda nake nema, Allah ya biya mana bukatun mu na alkhairi baki dayan mu*

*Dan Allah kar ku yi fushi, kun san ba hali na bane jan lokaci ban typing ba, na gode*

PAGE 25:



Rubutu ya gani mai d'an yawa,wanda bai saba gani ba,hakan ne  ya sanya shi juya wa wajen su Hajiya Mama ya ce,

"Sai da safen ku, bari na je na d'an huta"

Tafiyar shi ya yi, ba tare da ya jira jin me za su ce ba, ya na fita Ihsan na shiga, ta na tsallen murna,

"Lafiya ke kuma ki ke tsalle kamar wata d'an akuya sabuwar haihuwa?"

"Kira ni komai ma Hajiya Mama, aikin bokan Aunty Zaituna na ci, ko kun san yanzu haka waccan gajalar bata gida? Ya maida ta gidan ubale, ana can ana zare ido"

Shewa suka sanya, tare da tafawa da Tasneem, wadda duk inda ake neman mai farin ciki a wannan dare aka same ta a dasa aya kawai.

Hira suka yi ta yi, tare da fatan Allah ya sa ta tafi kenan ba za ta dawo ba har abada.

Sa'eed kuwa sai da ya kwanta, a gado a sashen Mahwish, sannan ya fara karanta saqon, kamar haka.

~Assalamu alaikum Baby na, ina fatan ka na lafiya? Ina fatan ka ci abinci ka yi wanka, Allah ya kare min kai zuma na, dan Allah ina neman alfarma a wajen ka, ka sawwaqe min wannan auren, tun da sauran soyayyar ka a zuciya ta, bana so a yi nasarar sake dasa min qin ka a rai na, na fara saba wa da soyayyar ka,da dad'in ta, ba na so a kwace min d'an abinda ya yi saura, dan Allah ka saurari roqo na, kar ka qi yi min wannan alfarmar~

Wani irin abu mai nauyi ya ji ya tokare masa qirjin shi, da sauri ya tashi ya zauna, dan kuwa da kyar ya ke shaqar numfashi, a gaggauce ya lalubi No wayar ta ya danna kira, ta d'an jima ta na ringing kafin ta dauka, sallama ta yi cikin Muryar ta mai daɗin sauraro.

"Assalamu alaikum"

"Wa'alaikumussalam, Mahwish anya ki na so na ci gaba da rayuwa kuwa? Ki na so ko zan rayu na rayu da lafiya a tare dani ba tare da cutar shanyewar b'arin jiki ta kama ni ba? Mahwish ko kin san kalaman ki daidai suke da kisan kai? Yanzu in da da qarar kwana na mutu fa? Za ki iya sanadin rayuwa ta ashe Mahwish?"

Tunda ya fara magana take kuka, cikin tsananin tausayin shi, dan kuwa duk abinda yake fada daga zuciyar shi yake sauka a saman labb'an shi,tafi kowa sanin yanda yake tsananin son ta da qaunar ta, ita ce farko a komai nashi, bai had'a ta da kowa ba, kalaman shi sun daki zuciyar ta iya duka, sun sa ta yi laushi har ta kasa ci gaba da roqon shi,

"Dan Allah ka dena irin wadannan kalaman masu kama da bankwana na har abada, bankwanan da zan rayu da tunanin ni ce ajalin ka, Yah Sa'eed ina son ka, ban san sanda na fara ba, ban san sanda zan dena ba, abinda na sani kawai shi ne, ina son ka, kai kadai ne a zuciya ta, a yanzu na tabbatar da cewa yanzu ne nake yin so, amma ka sanar da ni, ya zan yi? Ka na jin abubuwan dake faruwa fa, what if aka yi sanadin rayuwa ta?"

"Ba wanda ya isa ya dauki ran ki sai sanda Allah ya nufa, dan Allah ina so mu yi wani abu daya, me zai hana mu tashi mu yi sallah yau da daren nan, mu roqi Allah alkhairin tarayyar mu? In ba alkhairi na tabbata Allah ma ba zai sake had'a mu ba, dan Allah ki taimaka min mu yi hakan, duk abinda Allah ya zartar zan amshe shi da hannu bibbiyu"

MAHWISHWhere stories live. Discover now