MAHWISH PAGE 33

32 3 0
                                    

Da qarfi ta bud'e qofar ta shiga, burki ta ci da ta gan shi a zaune a bakin qofar d'akin Mahwish ya na kuka, ya na roqon a bud'e.

Cike da rashin kunya ta murgud'a baki, sanan ta ce,

"Yah Sa'eed Hajiya Mama ta ce tun da ka sake ta, kar ka shiga inda take, ka shiga d'akin ka anan za ka dinga kwana, in kuma ba haka ba, sai dai ka koma sashen mu ka dinga kwana har Tasneem ta dawo"

Ko kallon ta bai ba, ya miqe,ya koma kujera ya zauna, ya na share hawayen shi, a hankali ya bud'e baki ya ce mata,

"Fita ki bar nan"

Cikin rashin kunya da qunquni ta fita, tare da doka qofar kamar za ta balle ta, ta na zuwa ta sanar da Hajiya Mama abinda ta gani har da qari, ai kuwa Hajiya Mama sai ta sa kuka, ta ce,

"Ni Adama yau ina ganin halin d'an Adam, wai a ce na haifi d'an da ciki na, amma ya fifita mace a kai na,qaramar yarinya 'yar cikin shi ta dinga juya shi, to ba zan yarda da wannan iskancin ba,Allah ya kai mu ta gama iddar na ga yanda za ai ta ci gaba da zama anan ai"

Zugata Ihsan ta ci gaba da yi, ita kuma kamar sokuwa haka take d'aukan shawarwarin da 'yar cikin ta ke bata.

Su na nan zaune suka ga an kunna wutar d'akin Sa'eed d'in, murmushi Hajiya Mama ta yi, ta ce,

"Dan raini, ai na zaci ba zai koma can ba, yanzu in je na tattaro shi da kayan nashi ya dawo nan da zama"

Sa'eed kuwa ya na shiga ya fad'a kujerar dake cikin dakin ya kwanta, tare da lumshe idanun shi, hango Mahwish yake cikin qananan kayan ta,masu yi mata kyau, su fitar da duk wata sura ta jikin ta, iska ya shaqa, ya na tunano qamshin ta, da murmushin ta, da doguwar fuskar ta mai tsananin kyau.

Wani irin shauqin yake ji game da ita, ya na jin tsananin buqatuwa zuwa gare ta, tuna wa ya yi da shigar da ta yi d'azu, sai ya ji ya kasa jure wa, kamar wanda aka mintsina haka ya miqe, ya fita, a daidai wannan lokacin Mahwish na kitchen ta na had'awa Ludhfi Madara ya tashi ya na rikici.

Rungume ta Sa'eed ya yi da sauri, ya na sauke ajiyar zuciya, tare da shinshinar wuyan ta zuwa kafad'ar ta, rintse idanun ta tayi, ga magana a wuyan ta amma ta kasa fitar wa, sun jima a haka, ya na qoqarin kissing din ta ta na kauce wa, da kyar ta samu nasarar kwace jikin ta, ta dau madarar za ta gudu, riqe hannun ta ya yi, sannan ya ce,

"Mahwish ki taimaka min, kin san dai ba na iya kwana ba ke, ko Tasneem, kin kuma san irin son da nake maki, Dan Allah ki taimaka min"

Cikin rashin fahimta ta kalle shi ta ce,

"In taimaka maka? In taimaka maka fa ka ce, ni kuma tawa rayur ta fad'a cikin musiba ko? Ka ga malam sake ni, ni yanzu zaman idda nake, da na gama zan qara gaba, ba za ka sake gani ba, ba za ka sake ji na ba, zan maka nisa, nisa na har abada"

Da qarfi ta kwace hannun ta ta koma d'aki, ta na ba wa Ludhfi madara ta na kuka.

Jiki ba kwari haka ya koma nashi d'akin, qarshe dai kasa bacci ya yi, saboda ciwon mara, kanwa ya jiqa ya sha ya koma d'akin.

Cikin dare da ya ga baccin ya qi zuwa, kawai sai ya yi alwala ya yi sallah, ya yi ta addu'a har asuba.

Da sassafe Mahwish ta yi wanka, ta wa Ludhfi, ta zaunar da shi a daki, yaro ya saba ana wanka a fita, ya ga sun qi fita, da ya tabbata ba za ta bar shi fita ba sai ya dinga kuka.

Jin kukan shi ne ya sanya Ihsan zagayo wa ta shiga sashen Mahwish d'in, nan ma ta tarar da Sa'eed na ta kiran ta, akan ta ka masa yaron ya lallashe shi, taqi bud'e kofar,

"Yah Sa'eed Hajiya Mama ta ce ka je"

"To ki ce ina zuwa, Sarkin gulma me kuma ki ka ce nayi ? Kar ki na had'a ni da mahaifiya ta Ihsan, ban maki komai ba a rayuwa ta sai alkhairi"

MAHWISHWhere stories live. Discover now