Da kuka ta shiga gidan, kamar an yi mata rasuwa, hakan ne ya bawa Mahwish da ke ta shirya wa dan zuwa gaida Hajiya Mama damar leqawa ta window ta gan ta, ido hud'u suka yi, kafin Mahwish ta bar jikin window ta na ayyana kamannin matar a ranta, ta kusan sakin labulen ta,matar ta zabga mata harara, tare da buga wani dogon tsaki ta shige ciki, kyabe baki Mahwish ta yi, ta ci gaba da kafa kyakkyawan d'aurin d'anwalin da take yi.Riga da zani ne a jikin ta na leshi, mai kyau da tsada,ruwan zuma mai haske, ya yi mata kyau ba kad'an ba, sai baza qamshi take mai sanyi da dad'i, Sa'eed sai farin ciki yake, duk da ya san sai da ya roqa kamar zai kwanta kan ta amince, amma ya ji dad'i da ta amince za ta gaishe da mahaifiyar shi.
Qafar ta ta warke tsaf, ba inda ke mata ciwo yanzu, sai zuciyar ta, kalaman da Salim ya mata a daren ranar suna matuqar raunata dukkan gabb'an ta, ta yaya zai ce in bata balle auren Sa'eed ta aure shi ba zai nemi wata? Ashe dama soyayyar ta batai zurfi a zuciyar shi ba? Yaushe ma ta yi auren da har zai ce zai nemi wata? In a son ta ne ai ya sani ba za ta bari a aura mata wani ba shi ba, ita ta yi iya qoqarin da za ta yi dan su kasance tare, shi wane qoqari ya yi musu?
"Kin gama mu je?"
Banza ta yi da shi, ta dauki mayafin ta ta yi gaba, hannu ya d'aga ya duqa kad'an ya na murmushi, sai da ta fita sanan shima ya fita ya ja musu qofar, akan idon Tasneem suka wuce, itama ta na so ta je wajen Hajiya Mama dan ta ga wucewar Ihsan ta na kuka.
Jera wa suka yi sai wani manne wa Sa'eed take dan ta ba wa Mahwish haushi, shi kuma ya na ta basarwa, dan ya gane me take yi, Mahwish kuwa dariya ta yi, ta kalle ta ta ce,
"Wa ma ki ke da suna? Whatever your name is ke ki ka sani, ai hawa za ki ya goya ki, har can, sai na san mijin ki ne, wawuya kawai mara aji"
A harzuqe Tasneem ta zabura za ta yi magana, Sa'eed ya dakatar da ita, ta hanyar bata hakuri,shi dai ba ya fatan abinda zai rusa wannan tafiya da aka faro cikin mutunci, (a ganin shi wannan babbar alfarma ce ya samu)
Da sallama suka kwankwasa qofar, kalaman Hajiya Mama ne suka daki kunnuwan su,
"....bar dan buta uba, shege me zubin birrai, in banda ma Allah ya ci da shi, ai ke ba sa'ar auren shi bace,ga ki nan yarinya zubin shuwa,to kin dawo gida kenan, dan uwar shi ya kuskura ya zo nan gidan ya ga yanda ake rotse, fitinanniyar tsohuwar Legas zan koma na ci uwar shi, ya je ya ci gaba da zama da dangin shi su aura masa mata hud'u a rana d'aya amma 'yata ta fi qarfin zama da kishiya"
(sorry ina zagi ko? This is the first time a duk novels dina, if u ar reading my novel for the first time, amin afuwa, wani abun ya zama dole ne)
Tun kafin su zauna Sa'eed ya b'ata fuska ya ce,
"Haba Hajiya Mama, ya za ki ce haka? So ki ke wannan karon ma ta bar gidan miji saboda za a mata kishiya? Ita kad'ai ce mace? A gaskiya in akai haka ba a kyauta ba, yarinya qarama da aure har uku ashekara biyar? Kishiya kan ta aka fara? Wad'annan ba kishiyoyi bane, dan Allah Hajiya mama ki...."
"Dakata min kar raina ya b'aci yanzu in ci uban ka in kora fanta in baccin gajiya, ke tashi tashi ki juya ya kalle ki da kyau, ke ba kalar kishiya bace, (Tashi Ihsan ta yi ta na wata karairaya, ba shape ba kyawun azziqi, sai farar fata) wannan ta maka kama da wadda za ta yi zama da kishiya?"
"Hajiya Mama ki yi haquri, amma a gaskiya ba a kyauta ba in dai aka raba wannan auren ma, wancan auren kar ki manta har d'akin mai gadi ta babbaka wa wuta ta qone da sunan wai mai gadi ya mata munafurci wajen miji, ta sanya wa shanu da tumakin mijin wuta a raye, yaran miji na bacci ta tashi qone su gaba d'aya,bayan kuma ita ce ta tadda mata a gidan ta, amma tace ba zata zauna da kishiya ba, haka ake yi? Kuma kin san auren cin amana ta yi,duk ki ka daure mata gin**,mijin aminiyar ta saliha baiwar Allah macen kirki da kamala, amma ta ce ba za ta zauna da ita ba, amma dake Allah na tare da baiwar Allah dangin miji suka ce ba zata koma ba, aka sako ta, ta sake wani auren, yanzu ga wannan, duk ta kaso ta dawo, haba Hajiya Mama duka duka nawa Ihsan d'in take, shekara ashirin da uku aure uku, haba"

KAMU SEDANG MEMBACA
MAHWISH
RomansaQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........