(Last page)
Mahwish ce kwance a jikin Sa'eed ya na sosa mata kan ta da take jin ya dame ta da qaiqayi, idanun ta lumshe kamar mai jin bacci, hannun shi dayan wayar shi ce riqe ya na duba Facebook, ya na ganin abubuwan da duniya ke ciki, na siyasa, addini da rayuwar yau da gobe, abinda ya fi damun shi shine yanda tarbiyya ke ta sake tab'arbarewa a cikin al'ummar musulmi, idan arne ya aikata abu mara kyau, dama an saka ran zai aikata tunda ya butulcewa Allah ya bijire wa ubangijin shi, me ya sa za a dinga samun musulmai masu aikata manyan zunubai har a kafafen yad'a zumunta kamar su Facebook, WhatsApp, Twitter, da sauran su ba kunya ba tsoron Allah? Ko a iya friend request da yake samu ya na ganin tashin hankali, sunayen batsa muraran na masu mad'igo da luwad'i da zinace zinace gashi nan kaca-kaca, kamar ba iyaye ne suka haife su ba, gyara zaman shi ya yi sannan ya ce,
"Babyna"
Cikin jin dad'in sosa mata kan da yake yi, ido lumshe ta gyara kwanciyar ta ta sake shigewa jikin shi, sannan ta ce,
"Uhmmm?"
"Kin san ni sai yanzu nake sake jin dad'in yanda kwata kwata social media bata dame ki ba, ke dai a bar ki da hira da Zulai da Hajiya, shikenan, na sha duba wayar ki ba dan baincike ba ba kuma dan ina zargin ki ba, sai dan ya na da kyau a matsayi na na wanda Allah ya ba wa kiwon iyalin shi ya na da kyau na san me kk yi a wayar ki mata da dama sun halaka saboda wayoyin dake hannun su ba tare da sanin mazajen su ba,sannan kuma taba wayoyin junan mu ya zame mana ba komai bane ki dau waya ta na dauki taki, ban taba ganin wani abu mara kyau a wayar ki ba, hakan ba qaramin sanya ni farin ciki yake ba, kuma ina yawan sanya maki albarka a duk sanda na duba na ga komai lafiya lau a wayar ki, kin san me yasa nake maki wannan maganar? "
A daidai wannan lokacin ta bude idanun ta ta na sauraron shi, dan ta na son sanin me ya kawo wannan zancen,
" Ah ah sai ka sanar da ni"
"Mahwish duniyar nan ta zo qarshe, dan Allah ki taimaka min wajen kula da tarbiyyar yaran mu, ko su nawa Allah zai bamu, ku had'a kai da Sumayyah ku basu tarbiyyar da ko bayan ba mu zamu dinga samun lada mai gudana,Mahwish ina mamakin ina iyayen yaran da ke facebook suke, sannan mu a society muna tare da yara qanana da magidanta 'yan luwad'i bamu sani ba, matan mutane sun lalace da neman junan su ba a sani ba, yau na shiga na ga abubuwan da suka tadan hankali, yara ne ko manya ne Allah masani, amma dai a profile din su hotunan duk yara ne, ba abinda suke tallatawa sai luwad'i, wa' iyazubillah, kenan qananan yaran mu dake tasowa are not safe at all, tunda magabatan su sun dawo mana da aikin da ko dabbobi basa aikata shi, sun dawo mana da aikin da Allah yake fushi da aikata shi, al'arshin ubangiji ke girgiza a lokacin da ake aikata su, (Luwad'i da mad'igo) na rasa me ya sa iyayen yanzu ke sakaci kwarai,dan sun ba wa yara ilimi shikenan sai su ja hannayen su su nad'e, ba ruwan su da meke gudana a rayuwar yaran su, ilimi kawai baya hana yaro shaye shaye, ilimi kawai baya hana yaro neman mata ko neman maza tun yarinta har ya yi aure matar shi ta zo ta na shan wahala sakamakon mummunar tarbiyyar da aka masa,bawa yaro ilimi kada'ai baya hana shi zama dan kidnapping ko dan damfara da sauran munanan laifuka, tarbiyya da dasawa yaro tsoron Allah ta yanda ko kana nan ko baka nan zai kiyaye dokokin Allah, sannan komai girman d'an ka ko 'yar ka in sukai ba daidai ba ka nuna masu kuren su ka dawo da su kan hanya, shine mutum ya cika uwa ko uba na gari, ya Allah kar ka sa zuri'ar mu ta kasance daga irin wannan lalatacciyar zuri'a dake tasowa"
"Ameen zumana, ka san wani abu? Iyayen yanzu su fa gani suke burgewa ne mallaka wa yara qanana wayoyin zamani, manyan wayoyin da basu san ya yaran ke siyan data ba, wasu ma fa a kwana daya sai yarinya ta cinye 2GB saboda kallon Tiktok, ko shiga Instagram ko YouTube, ina ta sami kudin siyan datar? Sannan iyaye ba su san me yaran ke kalla ba in sun shiga wadannan wuraren, Yau ko a nera dari take samun data ina take samun nera darin? Is so unfortunate ka ga 'yar musulmi wai ke yin Tiktok, sai an magana ta ce bata posting nata video ai kalla kawai take, amma ai ki na kallon video wanda ya dace da wanda be dace ba, baki da karatun da zaki ne? Boko ko islamiyya? Shi yasa gaba daya kan yaran ba komi, ba ilimi na haqiqa sai zallan shirme ne a zuciyar su da kawunan su, sannan laifin iyayen ne ta bangaren kauda kai akan yaran su maza baligai, ka ga ni na jima ina ayyanawa a rai na in Ludhfi ya kai shekaru sha takwas zuwa sha tara ko ashirin, a nema masa mata yar mutunci a qalla mai shekara sha hud'u zuwa sha biyar, mu dau nauyin ciyar da su da wajen zaman su, tunda Allah ya hore mana hakan, su ci gaba da karatun su, ita mace yanzu zamani ya zo mana da online education ba dole sai ta fita ba, sanda za ta zana jarabawa mijin ta ya kai ta, su dawo, musulunci dama be bawa mace damar fita ba, wayayyu ne yan boko suke ganin tawaya ne da danne haqqin mace, sai kuma an samu zinace zinace su dora wa maza laifin hakan again, na san cewa ta wani bangaren dole ne take sa matan fita saboda ana buqatar su a wurare da dama musamman bangaren lafiya, kuma in mace bata fita ba wataqila ba zata samu abinda za ta ci da ita da yaran ta ba, amma in har mace ta san ana tsare mata komai ba aikin jinya ko aikin da ya zamana ana buqatar mata ba, barin yawan fita shi yafi saboda fadar Allah ce ba ta mutum ba, ka ga a haka za a samu raguwar lalacewar da ake ta faman yi tsakanin mata masu aure ma'aikata, sannan za a rage yawan yara dake aikata zina, saboda yaran yanzu na fara jin sha'awa da neman biyan buqatun su ko ta halin qaqa da qananan shekaru, ba kamar na da ba, to amma iyaye basa gane hakan, yaro ya balaga ya balage a gaban ka, ka san dai ba waliyyi ka haifa ba, kowa a duniya yana da sha'awa, amma ba a damu a san yaya yaran nan suke kawar da tasu ba, wayoyin matasan yanzu duk uwa ko uban da ya yi gangancin dauka ba tare da izinin yaran ba, dayan biyu ne, ko a samu bugun zuciya a wuce qiyama, ko a samu hawan jinin da zai raka mutum har kushewa, tabbas Abban Ludhfi sai mun dage, kuma mun tsaya tsayin daka wajen yin addu'a ma zuri'ar mu da dikkan musulmi, Allah ya sa mu dace, kuma inshaa Allahu zamu tsaya tsayin daka wajen kula da tarbiyyar yaran da Allah zai bamu da ni da Sumayyah"

ESTÁS LEYENDO
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........