Da kallo Xulaihah ke bin su, ta kasa fahimtar mai gaskiya a tsakanin su, Sa'eed ya ma rasa me zai ce, kawai sai ya fita, bai zame ko ina ba sai wani wajen cin abinci mai kyau, domin kuwa hasashen shi ya gama bashi Tasneem ba za ta yi abinci ba yau,ba zai fara tunkarar Hajiya Mama ba da lalurar dafa masu abinci, duk da dai akwai Iya, amma ba ya son tambayoyi.
Ya na tafe ya na tunanin kalaman Mahwish, daga baya abun ya dena bashi haushi da mamaki, ya koma bashi dariya, musamman in ya tuna yanda take tura baki a lokacin da ta taqarqare ta na zuba masa sharri.
A can gidan Sa'eed kuwa Mahwish ta balbale Xulaihah da fad'a, wai saboda me ya sa ta sanar da ita halin da take ciki ba ta yi wani yunkurin daukan mataki ba, cikin nutsuwa Xulaihah ta ce,
"Yah Mahwish da ga yanda ki ke abubuwa na tabbata shirya magana kawai ki kai, na sani ni yarinya ce, amma kuma da hankali na ai, kin ce an maki fyade,in hasashe na ya yi daidai da duk abinda na gani, tun zuwa na, kokawa ku ka yi, saboda kin hana shi haqqin shi har ku ka fasa kayan d'akin ki, in haka ne kuwa ke ce babbar mai laifi, shi kuma tunda kin qi yarda da ya hakura lokaci na nan da za ki kai kan k....."
"In kai kai na gidan uban wa? Xulaihah in kai kai na gidan uban wa? Ashe dama baki da mutunci? To hasashen ki bai daidai ba, bayan ya gama min abinda zai min ne, takaici ya sa na fasa komai, ahir din ki da min fatan kai kaina wajen Sa'eed, har abada haka ba za ta faru ba,"
Ta na gama fadan hakan ta murguda baki ta juya wa Xulaihah baya ta yi kwanciyar ta, Xulaihah na tsaye ta na mamakin tsaurin ido da taurin kai irin na Mahwish, a tunanin ta ai komai ya wuce, auren Sa'eed muqaddari ne daga Allah,qaddara kuwa ta riga fata, to mene ne na d'aga hankali haka?
Zama ta yi a gefen Mahwish d'in za ta yi magana suka ji sallama, Xulaihah ce ta leqa, sai ta yi ido biyu da Hajiya Mama, duk da cewar ba su taba haduwa ba, amma kamannin su da Sa'eed ya bayyana ko ita wace ce, dan haka har qasa Xulaihah ta durqusa ta gaida ta.
Ita kuwa Hajiya Mama a ran ta ta na ayyana,
'Da daddare na gan ta 'yar kubul-bul kyakkyawa, fara tassss, amma yanzu sai na gan ta 'yar firit ko qugun azziqi bata gama mallaka ba balle nono, ohhh wannan zamani da muke ciki komai sai an masa ha'incin
Ta na tsaka da tunani Xulaihah ta ce mata,
"Bismillah Hajiya, Yah Mahwish din na ciki"
Da sauri Hajiya ta wangale vaki ta na fad'in,
"Yauwa ko da na ji, haka kawai yaro ya auro dandatsetsiya na ga an sauya masa, ita ba za ta fito ba kenan, sai dai in shiga, da kyau....ina shi Sa'eed din yake,sannan ke kuma wace ce? Daga ina?"
Wajen zama Xulaihah ta ba wa Hajiya Mama sannan ta zauna a qasa, ta ce,
"Yah Sa'eed ya d'an fita, ni qanwar Yah Mahwish ce"
"Tooo ikon Allah, har an fara zuwa gidan d'ana da asussuba kenan, ko anan ki ka kwan ne baiwar Allah?"
Kallon ta Xulaihah ta yi, ta ga yanda Hajiya Mama ke bin ta da wani irin kallo, sai ta ji gaban ta ya fad'i, anya Mahwish za su daidaita da matar nan? Sam bata ga alama ba.
"Yah Mahwish ba ta da lafiya ne shi ne da safe Yah Sa'eed ya ce na zo na kula da ita"
Zabura Hajiya Mama ta yi kamar bata san me ke faruwa ba,
"Me ya same ta? Ba a fad'an ba sai an yo gayya?"
Wani iri Xulaihah ta ji, ita din ce gayya?
"Ta d'an ji ciwo ne, amma an d'inke wajen, ta samu ta yi wanka, ta yi sallah ta koma bacci"
Qanqance idanun ta ta yi,ta na nazarin kalaman Xulaihah,
"Ke d'in yaya sunan ki? Dan ni na fi sanin yaran Sageeru, tunda shi ne abokin miji na, Yaran Farouqu ban san ku ba, gwanda ma Hajiyar taku mun har had'u da ita"
VOUS LISEZ
MAHWISH
Roman d'amourQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........