MAHWISH PAGE 22

44 4 0
                                    


Ta na bud'e wa Ihsan ta bangaje ta ta shige, ta na yatsina da rashin mutunci, dakewa ta yi, ta koma gaban Ihsan din cikin wani irin qarfin hali, ta ce,

"Ke Maman Bilal, in kin San ba alkhairi ne ya kawo ki ba, ki kama hanya ki bar nan, in ba haka ba, zan nuna maki d'aya daga kalar rashin mutunci na, da ya dame nake sau goma, na kula ku ba ku san mutunci ba ko? Ba kusan a muku zuru ba ko?"

Tabbas Mahwish ta bala'in tsorata Ihsan, dan kuwa yanayin da ta yi magana da shi, yanayi ne na ba wasa,tsaki Ihsan ta yi, ta kama.hanya za ta fita, har ta kai qofa ta juya ta kalli Mahwish ta ce,

"Ba dai kin dage sai kin zauna a gidan nan ba? Ba dai kin nace kin liqe sai kin zauna a gidan nan ba? To ina maki albishir da zaman qunci zaman tashin hankali da nadama,ke na qabari ma sai ya fiki jin dad'in rayuwa Mahwish, mu zuba mu gani, za ki ce na fad'a maki wanan maganar"

A bude ta bar qofar ta yi ficewar ta gantalin ta,  dan yanzu abun ya qara yawa, sam sam ba ta son zaman gida, ta fi so ta bazama kamar balama, neman samari, gashi duk wanda take samowa 'yan a sha love ne, ba 'yan a yi aure ba, wannan yanayin da take ciki bai ishe ta ishara ba, amma take so ta lalata zaman auren wata a gidan mijin ta.

Satin Mahwish d'aya da dawowa, Tasneem ta dawo,dan haka girki ya koma hannun ta kenan, Sa'eed ji yake kamar ya rasa wani bangare na jikin shi,a lokacin da zai koma wajen Tasneem, Mahwish ma haka, amma haka suka ba wa junan su hakuri suka rabu.

A lokacin da Sa'eed ya gama kwana biyun shi a wajen Tasneem, sai ta buga qasa tace ai sai ya rama mata duk kwanakin da ya yi da Mahwish da bata nan, wani mugun kallo ya mata, sannan ya ce,

"Tasneem ki bi Ni a hankali, gaf nake da na tsinke igiyar da ta daure ki a jiki na, ke wawuya ce ba ki san ciwon kan ki ba, ina kyale ki ne saboda zumunci da kuma Hajiya Mama, banda haka da tuni na yakice auren ki na huta, dan ba abinda yake amfana ta da shi,Tasneem a matsayi na na mijin da ki ke ikirarin ki na so kuma a qarqashin iko na ki ke, ba zaman kan ki kike yi ba, ina kwance gadon asibiti ki ka kama hanya ki ka bar gari da sunan kin tafi biki, wa ki ka tambaya? Ke in ba ma qarfin imani ba taya ki ke so na yarda da ke, har na ci gaba da mu'amalar aure da ke? Tunda na san ya halin ki yake tun kafin aure, banda tabbacin ina ki ka je, da wa ki ka had'u, sannan yanzu ki zo ki na min maganar banza maganar wofi,"

"An yi maka maganar banzan Sa'eed, na ce an yi maka maganar banzan, ba inda za ka tafi ka bar ni sai ka biya ni kwanaki na da bana nan, wani ya sa ka kwanciya asibi da da za ka fake da halayyata ta baya ka ci mutunci na?"

"Ke jahilar ina ce da ki ke maganar biya maki kwanan ki? Dama haka musulunci ya ce in mace ta yi tafiya sai an rama mata kwanakin ta? Dalla Malama matsa ki bani waje,wannan na d'aya daga dalilin da ya sa na saki a islamiyya tun ki na qarama amma se ki ka gudu, ba ki nan ba ki can, da aure ma na sa ki a islamiyyar matan aure kin qi zuwa, to matsa min na wuce kafin na sab'a maki"

Matsa wa ta yi, ya wuce, ita kuma ta dinga zazzaga masa rashin mutunci, ta na fad'a masa duk wata magana da ta zo bakin ta, ya na fita daga sashen ta ya kalli sashen Mahwish sai ya ji wata iriyar natsuwa da kwanciyar hankali na ziyartar shi, sai ya ji kamar ya fita daga duhu,zai fad'a haske, da sassarfa ya qarasa sashen nata, ya so a ce qofa a bude take ba sai ya kwankwasa ba.

Ya na shiga ya gan ta tare da Xulaihah da wasu 'yan mata biyu, duk dai su na kama, da dukkan alamu 'yan uwan su ne.

Ta na dora ido akan shi, ta ji wata nutsuwa ta saukar mata, da sauri ta miqe kamar za ta wajen shi, sai ta dakata saboda baqi, Sa'eed kuwa yi ya yi kamar bai gan su ba, ya kasa jure zillon da zuciyar shi ke masa akan masoyiyar shi, mai kula da dukkan buqatun shi, mai masa ladabi da biyayya, duk da ya san har yanzu soyayyar da take masa bata kai rabin tashi ba.

Rungume ta ya yi, tare da sauke ajiyar zuciya mai qarfi, shafa bayan shi ta yi a hankali, ta rad'a masa,

"Ka ga qanne na fa su na kallon mu"

MAHWISHOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz