Zaman Mahwish a gida ya sa ta ji sauqi sosai, ta warware, kuma ta na samu ta ci abinci, duk da ba kowanne ba, sai ta zaba,amma dai ta na ci ba kamar da ba, kwana biyu na cika, Xulaihah ta raka ta asibiti, dircet scanning Dr. Abubakar ya ce za a yi, a ga me ke sanya ta ciwon marar.
Ta na zaune ta na ta zuqar ruwa,dan ta ce ba ta jin fitsari, Sa'eed ya isa wajen, kallon shi ta yi, ta dauke kai, tare da nuna bata so ganin shi ba a zahiri, amma cikin ran ta, ta yi matuqar farin cikin ganin shi, ta wani bangaren kuma ta yi baqin cikin ganin shi a rame kamar ya yi jinya, sake kallon shi ta yi ta qasan gashin idanun ta, ta ga shi ma ita yake kallo, da kyar ta had'iye ruwan da ke bakin ta, zama ya yi kusa da ita, ba tare da ya daina kallon ta ba ya ce,
"Mahwish, dan Allah, ki yafe min, duk abinda na maki, ki dena azabtar da zuciya ta, da gangar jiki na, Mahwish kin san matsayin ki a waje na, har yanzu bai sauya ba, hasali ma ninkuwa soyayyar ki take yi a zuciya ta, ke d'in jaruma ce, mai......"
"Ka ga sweet talker ,kar ka zo nan ka na min dadin baki, ba a location d'in daukan Film ake ba, lafiya na zo nema a asibiti, Yah Sa'eed me ye laifi na ne? Mene ne laifi na dan kawai ina son ka, ina so na zauna da kai a matsayin mijin auren Sunnah ba zaman da Allah ya hana ba? Ban musu komai ba, amma....."
Kuka ne sosai ya kama ta, da sauri ta haye gadon da za a mata scanning, cikin kuka ta ce,
"Dan Allah ka duba ni, in koma gidan mu, in kuma ba zai samu ba, sai na sauya wani wajen,"
"Mahwish da..."
"Kar ka ce komai Yah Sa'eed, Allah ya sani daga farkon haduwa ta da kai, har na baro gidan ka, ba ka taba min komai na rashin kyautata wa ba, amma mahaifiyar ka, da yayar ka, da qanwar ka, da matar ka, duk akai na? Ni kad'ai? Da qananan shekaru na? Me na musu? Dan Allah ka bar ni ka sawwaqe min wannan auren,kai ka huta, Ni ma na huta"
"Dan Allah ku bar wannan maganar mu ga me ke damun ta, in an gama sai ku je can office d'ina ku tattauna, kun ga nan mutane na jira a can waje, ok?"
Sa'eed ne ya daga kai, ya ce,
"Ok,"
Mahwish na ta sharar hawaye, aka fara scanning, Sa'eed ba abinda yake sai kallon zubar hawayen ta, ya na jin wani irin zafi a zuciyar shi, ba ya so sam ya ga b'acin rai a tare da ita, balle hawayen ta, ji yake kamar ya zare mata duk wata damuwar ta, ya goge duk wani tunanin abinda ya faru a baya daga zuciyar ta, amma ba shi da wannan ikon.
Abubakar ne ya juya ya kalle su baki daya cikin farin ciki, sannan ya ce,
"Masha Allah, Alhamdu lilLAAH, congratulations man, she is pregnant,"
Cike da wata iriyar murna Sa'eed ya isa gaban na'urar ya na duba wa, dan ya tabbatar, ya na ganin hoton alamun d'a a jikin na'urar kawai sai ya ja baya, ya tsugunna, ya yi sujjada domin gode wa Allah subhanahu wata'ala,akan kyautar da ya masa, bayan shekara da shekaru da yin aure, har ya fara tunanin ko zai je a duba shi ne, ko ya na da matsala, ashe ba shi da matsalar komai, hamdala ya dinga yi, Xulaihah da Mahwish ma haka.
Sa'eed ne ya isa ga Mahwish wadda ke gyara zanin ta za ta sauka daga gadon, da sauri ya rungume ta, ya na masu barkar samun qaruwa, cikin gaggawa ta rungume shi itama, ta na mai nuna farin ciki da godiya ga Allah, da wannan kyakkyawar kyauta da ya mata.
Tuni suka manta da fadan da ke tsakanin su, su ka tsaya jiran bayani daga bakin likita bokan turai.
Dr. Abubakar ya sanar da su cewar cikin ya kai watanni uku da sati biyu kenan, ya kuma sanar da su duk abinda ya dace ta kiyaye, da wanda ya dace ta dinga yi.
Godiya suka yi wa Abubakar suka tafi, gidan su Mahwish suka je, Xulaihah ce ta ba wa Hajiya kyakkyawan albishir d'in samun jika, hamdala Hajiya ta dinga yi, sannan ta roqe su kar su sanar da Abban su, ita za ta masa albishir.
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........