*To yanzuuu in na hwara gabatar da uzurina da na sanar da kuuuu ya za ai?😂 Ashe ba za a d'agan leg ba in d'an dinga fashi😂*
PAGE 29:
A kishingid'e ta tadda Hajiya Mama ta na kallo, kamar ba abinda ya dame ta a duniya, zama ta yi a gefen ta ta zabga ajiyar zuciya, irin ta mutanen da suka so gulma, sannan ta ce,
"Hajiya Mama ki na nan zaune za a yi aika aika, wani mummunan lamari na shirin faruwa, ke baki sani ba,"
A zabure Hajiya Mama ta miqe daga kishingid'ar da ta yi, ta ce,
"Me ya faru? Gidan wuta ne za su yi yajin aiki, ko na ruwa ?"
Dan guntun tsaki Ihsan ta yi sannan ta ce,
"Ke Hajiya Mama ana nuna maki Annabi amma sai ki dinga rintse idanun ki"
"Uwar ki 'Yar Aba ce ta nunan shi na rintse idon, kin ga kar ki had'a ni da Allah, bana so, ki sanar da ni abinda ke faruwa kai tsaye, bana son kwana, garin shegen jan ran ki za ki sa mu yi sab'o,"
"Allah na tuba Hajiya Mama ai mu sai dai Allah ya mana rahama kawai,.....uhmmm baki san me ke faruwa ba a gidan nan,"
"Me ya faru? Zan ci uban ki Sile na Jahun, za ki yi sauri ki fad'an me ke faruwa ko ba hali in maida kai nai kallo na?"
"Hajiya Mama ni fa ina zargin Mahwish ciki ne da ita"
Wata iriyar zabura Hajiya Mama ta yi kamar za ta kife a qasa, sannan ta daidaici cinyar Ihsan da ta kwakkwaye saboda son isar da gulma, ta d'asa mata wani irin duka, fuskar ta tayi jawur ta ce,
"Zan ci uwar ki duk sanda ki ka sake zuwar min da wannan wasan banzan, kar ki ga ana wasa ana dariya dake, ke baki da aiki sai mugun fata, in samu jika a wajen waccan in ce na samu me? To ahir din ki"
Cikin kuka Ihsan ta ce,
"Ai se ki bari gobe ta yi a tabbatar ko? Ba wai ki min irin dukan nan ba kuma magana ta ta tabbata"
Wani dukan Hajiya Mama ta kai wa Ihsan, amma bata same ta ba, dan kuwa ta hantsila ta gudu d'aki,
"Kin ga shegen bakin ki shi ne zai jawo mana masifa, ke da ba kya ganin zare ki kyale sai kin tsinka, yawan surutun ki, ni dai ya zamar min bala'i,"
Kai kawo Hajiya Mama ta fara a parlour'n, ta na nazari, a tsorace ta juya, inda ta ji wayar ta na qara, dauka ta yi ta duba sunan Zaituna ne a jiki, hannu na rawa ta amsa, ba sallama ba komai ta ce,
"Ke Zaituna, kin ji waccan yarinyar mai baqin mugun baki, wai ta na zargin kamar Mashawi ciki gare ta? To ni Adama in yarinyar can ta fara zuba kwai a gidan nan ai ranar fafa zan sha wahala, dan kuwa bamu san irin albarkar kwayayan nata ba, ko su yi yawa ko su yi kad'an,ko a haifi zakaru ko asamu kaji irin mu, to koma dai mene ne ai ba riba, dan kuwa kasafin hatsin mu zai ragu, ko ya ki ka ce?"
"Wannan shi ne dalilin da ya sa na kira ki, to ya zama dole a san yanda za a yi da wannan lamarin, dan kuwa ba zan tab'a bari, a rage min abincin kwano na ba, dama waccan sokuwar na zubi ne itama, wataqila da mun yi kwasa mai yawa, amma inaaa tun zubar da cikin nan da akai, an tabbatar mana da ba zata sake samun wani cikin ba, "
"Yanzu ba wannan ba, ya kamata tun yanzu ki yi wa boka waya, kafin gobe mu je, kin san su ba bacci suke ba, an amshi aikin mutane, gobe da sassafe dama bakwai ta miki wajen shi, ki je ko nawa ne ya kama ki yi magana zan turo Maki"
"To Hajiya Mama an gama"
Ji ta yi hankalin ta ya kwanta, dan kuwa ta san buqatar ta za ta biya, (subhanallah, ta yi wa boka imani, da yardar da mutum mumini ya kamata ya wa Allah, in ka sanar da Allah damuwar ka, ba a so a ci gaba da samun ka da wannan damuwar, tunda ka kai ta inda za a maka maganin ta me zai sa ka ci gaba da sa kan ka a cikin damuwa?)
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........