MAHWISH PAGE 45

32 2 0
                                    


*Assalamu alaikum my biyutiful mutane, ina fatan kun yi sallah lafiya? Allah ya amsa mana ibadun mu, Allah ya sa mu na cikin bayin shi da ya gafarta wa a wannan shekara, Allah ya maimaita mana, ya qare mu da lafiya da imani,Ameen*

Ta na shiga su Sumy fara da Sumy baqa suka taso suka tarbe ta, cike da fara'a, gaba d'aya hankalin ta ba ya jikin ta, jin ta take kamar wata sabuwar halitta.

Ko gaisa wa ba su yi ba, ta taka da kan ta, ta dauki cup d'in da suka zuba abubuwan maye a ciki, kamar wadda aka sanar mene ne a ciki, haka ta d'aga kai ta kwankwad'e, ba jima wa kuwa ta ji kan ta na juya wa kamar ba a jikin ta yake ba, dariya su sumy suka sanya, tare da tafawa,

"Mun samu new comer ,shi iskanci ba gadon shi ake ba, kana daga zaune in iskar duniya ta buge ka sai ka koma d'an ta"

Dariya suka sake sanya wa, suka tafa, sannan suka zauna kusa da Mahwish da ke gani double double, sumy baqa ce ta dafa ta ta ce,

" 'yar uwa lafiya ki ke kuwa? Da alama dai ke 'yar hannu ce ko?"

Sumy fara ce ta ce,

"Habaa ai da ganin wannan new comer ce, yau ta fara,"

Hannu Mahwish ta d'aga ta hau juya shi, tare da qoqarin yin magana, irin yanda 'yan maye suke yi,"

"Qara min wannan lemon in shaaa"

Jiki na rawa Sumy baqa ta dauki kwalbar barasan da suka yi wa wasu had'e had'en na maye ta tsiyaya wa Mahwish, za ta zuba mata wasu tarkacen Sumy fara ta riqe hannun ta ta ce,

"Da dukkan alamu farkon yin ta kenan, kar ki zuba mata abinda zai fi qarfin kan ta, bata daidai ita, na sabbin shigowa harkar"

Cikin dariya Sumy baqa ta ce,

"Shegiya sweetheart, wato so ki ke ta kamu sosai, a mata had'in gobe ki dawo"

"Kwarai da gaske,"

Su na dariya su na hira, suka dinga d'ura wa Mahwish kayan maye kala kala, dan kuwa ko sun hana ta, sai ta zabura ta dau wani abun, sunyi sunyi su hana ta, amma sun kasa, dole su ka kyale ta, qarshe dai kwashe komai suka yi, dan su kan su abun ya basu tsoro, kamar wadda ake ingizawa, sannan su da suka jima ma su na harkar basu sha abinda ta sha ba a ranar.

A nan Mahwish ta kwana, har ta wuni, maqotan ta na azziqi sun yi ta sintiri ba su gan ta ba, sai suka yi zaton kewar Sa'eed ke damun ta shi ya sa ta kulle kanta ba ta so a dame ta, dan kuwa har parlour suke shiga su yi ta sallama ba ta amsa su ba.

Hakan ne ya basu tabbacin ta na nan, kula su ne kawai ba ta so ta yi, dariya suka dinga yi, su na jinjina soyayyar da ke tsakanin ma'auratan, a kwana na uku ne, abun ya basu tsoro sosai, kar dai ta mutu ne, to ta mutu ai da za a ji warin gawa, to ko tare suka tafi? Amma ba sallama kuma shi sa'eed bai gaya wa mazan su ba.

Su na tsaka da tunani, da neman mafita, suka gan ta, ta fito daga gidan su Sumy ta na tafe ta na had'e hanya, ta na kuka, dan kuwa hankalin ta ya dawo gare ta, ta gan ta ta na zuqar sigari, shi ne dalilin kukan nata, sannan ta fito, sai tambayar ta suke lafiya? Amma ta qi kula su, ta wuce gidan ta.

Mamaki da tsoro ne ya bayyana a fuskokin maqotan ta, me za su gani haka?

Da sauri suka tarbe ta suka qarasa shiga da ita cikin gidan ta, su ka hau tambayar ta lafiya?

Ba baki sai kuka, ita kan ta ba ta san me za ta ce ba, sannan bata san ta ina za ta fara musu bayanin abinda ke faruwa ba,saboda ita ma bata san me ke faruwa ba, kawai ta san hankalin ta ya gushe na wani lokacin da bata san iyakar shi ba, kuma ya dawo gare ta, ta na mai aikata mummunar d'abi'ar shaye shaye.

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, hasbunallahu wa ni'imal wakil, lahaula wala quwwata illa billah"

Tasbihi kawai take ga Allah, ta kasa gane me ke faruwa, kan ta ya d'aure, zuciyar ta da ƙwaƙwalwar ta sun cushe da tunani kala kala, me ye gamin ta da shaye shaye kuma?

MAHWISHحيث تعيش القصص. اكتشف الآن