Dayar wayar shi ta miqa masa, ta masa nuni, da tun da ya fita ake kira, ganin ran ta bai b'aci ba, ba wata alamar ta ji wayar da yake yi, sai ya ji hankalin shi ya kwanta, wata sassanyar ajiyar zuciya ya sauke, ya mata yaqe, ya qara nesanta kan shi da ita, ta na ganin ba ya so ta ji wayar da yake, sai ita ma ta bar wajen gaba d'aya.
Cikin qasa da murya ya ce,
"Hajiya Mama wane irin aure kuma? Ba zan iya ba gaskiya, ki na gani yarinyar nan Tasneem ta ma bar inda ku ke, dole in na zo sai na je wajen ta, ga wajen ku, ga nan,nawa zan kasa kai na to? Abun zai min yawa"
'Ka kasa kan ka dubu ma, bai dame ni ba, dole ne ka yi abinda na sanya ka'
Kashe wayar ta yi, ta na surutai, Sa'eed kuwa zama ya yi a qasa, sai ga hawaye na bin kuncin shi, wai me ya wa mahaifiyar shi da zafi ne haka? Iya biyayya da kyautata wa ya na mata, amma me ya sa take masa haka?
Ba shi da amsar tambayoyin shi, dan haka ya miqe ya shiga ciki, jiki ba kwari ya kwanta tare da rintse idon shi, Mahwish kuwa da ta ga haka, sai ta kama kan ta, dan ba ta son ta yi jassasa, in ya so fada mata zai fada mata ko ma me ke damun shi,yanzu bari ta bar shi ya yi bacci.
Abu kamar wasa, sai da suka yi sati biyu Sa'eed bai je gida Weekend ba,kuma Hajiya Mama da Zaituna ba su dena damun shi akan ya je ya ga Mommy ba,ya na son zuwa amma tsoro ya ke ya je a kira ta su hadu, dan halin Hajiya Mama ba wanda bai sani ba,ko kuma ta na iya tursasa shi ya je kan dole.
A cikin sati na uku ne Hajiya Mama da Zaituna suka matsa masa, akan sai ya je, Mahwish ma da kan ta, ta ke tambayar shi me ya sa ba za shi gida ba? Kar ya manta fa ya na da wata matar, ga mahaifiyar shi.
Shiru ya yi ya na kallon ta, can kuma ya sauke idon shi qasa, ya ce,
"Da za ki san dalilin da ya sa nake gudun gida, tabbas da kin ban tukuici mai tsoka"
"Ni kuwa mai zai sa na baka tukuici mai qashi ma, balle mai tsoka, akan tauye haqqin wasu?"
"Mahwish haqqin ki ake so a tauye, ba wai ke ce za ki tauye haqqin wasu ba, Hajiya mama....uhmm...Hajiya Mama, aure ta ke so na qara"
Mahwish ji ta yi kamar ta dena ji na wasu seconds, sannan kuma ta dena gani, wanne irin aure,ta jima kafin nutsuwar ta ta dawo gare ta, dan haka cikin sanyin murya ta ce,
"Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi, ya bamu zaman lafiya"
Sa'eed baki ya bud'e, ya na bin ta da kallo, har za ta bar wajen, ta maida bowl din da suka gama shan fruit salad kitchen,ya ja hannun ta, ya zaunar da ita saman qafar shi, ya na kallon kwayar idon ta,wanda a da suke fari tas, amma a yanzu ya koma jawur, kuma ba d'igon hawaye a ciki.
"Mahwish baki ji me na ce bane! Aure fa suke so na yi !"
"Baby na ji ka sarai, me zan ce to da ya fi addu'a da neman zabin Allah a ciki? Ni ba zan takura wa kai na ba, ba kuma zan takura maka ba, mu hadu mu sa ka cikin damuwa,dan haka in ka na ganin ka na so, ba matsala ka qara auren, Allah ya bamu zaman lafiya, abu daya nake so da kai shi ne,ka tabbatar ka tsaida adalci a tsakanin mu"
Kafin ya ce wani abu ta bar wajen, ta na shiga kitchen ta ajiye bowl din ta dafe sink ta dinga kuka mai tsananin ban tausayi, ta jima sosai ta na kuka, ba tare da ta san Sa'eed na tsaye a bakin kofa ya na kallon ta ba, shi ma hawayen ne ke zamubar masa.
A hankali ya taka ya rungume ta, ta na jin shi a jikin ta ta juya itama ta rungume shi ta na kuka sosai, Sa'eed bai san da bakin da zai lallashe ta ba ma, dan haka tsaya wa ya yi a wajen, ya na shafa bayan ta, har sai da ta daina kukan, sannan su ka koma parlour.
Tattauna wa suka dinga yi a game da auren, Mahwish ji take kamar zuciyar ta ta fito, dan azabar da take ji, ashe dama haka take son Sa'eed ba ta sani ba, ita tunda take bata tab'a daukan Tasneem a wata tsiya ba, dan kwata kwata bata gaban Sa'eed, amma ta na tsoron kar Hajiya Mama ta aura masa wadda ta fi Tasneem rashin kan gado, a zo a hadu a sa ta a uku, shiru ta yi, ta na tunani, Sa'eed ya ce,
YOU ARE READING
MAHWISH
RomanceQiyayya mai zafi ta juye zuwa zazzafar soyayyar da tai sanadin sanya Mahwish jure duk wata musibar rayuwa akan soyayyar ta........