MAHWISH PAGE 37

26 4 0
                                    


Tashi ta yi zaune ta kalli Farhan, tare da amsa masa sallamar shi, ba tare da ya gaishe ta ba, ya na murmushi, irin na yara masu kunyar nan, in su na son mutum, ya miqa mata kwano, amsa ta yi ita ma ta na murmushi ta ce,

"Farhan d'ina kenan, Sarkin kunya, maman ka ce ta ce ka kawo min? Ina godiya sosai, jira ni na kawo maka tukuici, domin bahaushe ya ce yaba kyauta tukuici, irin wannan kayan dad'i haka?"

Tafe take ta na magana, ta na duba soyayyar kazar da take kyautata zato daga wajen Maman Farhan take, tsaya wa ta yi cak a daidai lokacin da ta dauki yanka d'aya za ta kai bakin ta, kalaman shi suka doki kukkuwan ta.

"Ba Mamana bace ta dafa, Maman Bilal ce ta kai wa Mamana ta ce na kawo maki, in ce mama na ce ta ce in kawo, kar in ce Maman Bilal ce, (Ihsan kenan)"

Da sauri ta mayar da naman ta na zare ido, mamaki da kuma mugun tsoro ne ya sanya  ta ajiye kwanon da sauri, ta isa gaban shi, ta durqusa ta sake tambayar yaron, nan dai ya jaddada mata ba maman shi bace ta soya, Ihsan ce ta kai, ta ce a ce Maman Farhan ce ta bayar.

Wato sun ga ta dena cin komai na wajen su, Sa'eed ya hana ta, itama ta yi alqawarin ba za ta sake cin abun su ba, tunda ba su qaunar ta, shi ne suka biyo ta hannun matar da ta yarda da ita, ake so a had'a baki da ita a cutar da ita kuma.

Tabbas rayuwa abun tsoro ce, kuma ko za ta rantse ba za ta yi kaffara ba, ta san akwai wani mugun abun da aka qulla, bata fasa ba wa Farhan tukuici ba, ta ce ya ce wa mamar ta shi ta na godiya sosai.

Ya na fita ta tafi dust bin ta zubar,dan ba za ta iya ci ba, ta tsorata kwarai da lamarin su, sun dage sai sun cutar da ita ko ta halin qaqa.

Bayan ta dawo natsuwar ta ne ta ke sanar da Xulaihah abinda ya faru, shawarar riqe addu'a da ibada ta bata, dan kuwa ta na buqatar su a cikin wadannan azzaluman mutanen.

Cikin Mahwish har ya fara girma wani gagarumar nasara ta same su, dan kuwa Sa'eed ya sake bude wani super market din da ya fi wannan girma a cikin garin na kano, tsakanin tsohon super market din shi da gidan su akwai nisa sosai da gaske, kuma wajen na da buqatar shi dan samun hab'akar kasuwancin,tun ana ginin wajen ya sa a gina masa gida madaidaici a bayan super market din, duk a tare aka gina, akai komai, Hajiya Mama ta so zuwa ta ga waje, a ranar da za a bud'e wajen, har walima se da ta yi ta na ta wa qawayen ta d'agun kai, ita a dole uwar mai azziqi,amma Zaituna sai ta ce ta bari sanda ta ji sauqi su je can d'in tare, Hajiya Mama na ji na gani taqi zuwa, saboda zaituna ta ce kar ta je.

Sa'eed ya sanar da iyalan shi duka biyun, su shirya da su za a je, a ga sabon waje, zai je ya dakko Ludhfi daga gidan Hajiyar Mahwish, a tafi da shi.

Tasneem da ke cikin tashin hankali cikin Mahwish ya kai har wata biyar bai zube ba, duk qoqarin su, ta ce ba za ta ba, dan kuwa ta na da abun yi.

Sa'eed ya ji tsananin takaicin abun nan, amma dole ya hakura, ya kasa mata fad'a ko ya yi sa'in sa da ita, Dan haka daga shi sai Mahwish, suka shirya za su tafi.

Har sun shiga Mota, Hajiya Mama ta aika a kira mata shi, ya na zuwa tun kan ya kai ga duqa wa a gaban ta, ta dakatar da shi,tace,

"Wato dan ka nuna wa duniya Mahaifiyar ka da 'yan uwan ka ba za su samu damar zuwa ba, ka dau matar ka za ka je da ita? Ba za ta iya hakuri ba ashe, kamar yanda muka yi hakuri muma duk da mu na so mu je? Ai kai ma ka sani Sa'eed in ba dan dole ba, ba abinda zai sa ba za mu je ba ko? Dan haka ba inda za ta itama,kai ko tausayin yayar ka ba ka ji, ka duba ka gani, ta samu ciki a wannan shekarun nata, ga uban laulayi sai da aka dawo da ita gida, tun safe bata iya fito wa ko da parlour ne, ka shigo baka tambaye ta ba ma, ka na zumud'i za ka fita da matar ka, sai ka ce ta koma, ba yanzu ba, ka tafi kai d'aya,ka je fatan alkhairi na da addu'a ta, da sanya war albarka ta duk su na tare da kai d'an albarka, Allah ya qara daukaka ka, ya kare ka daga sharrin baki da mutane"

MAHWISHWhere stories live. Discover now