MAHWISH PART 2 PAGE PAGE 9

45 7 3
                                        

MAHWISH PART 2 PAGE 9

HAERMEEBRAERH

Tun daga shiga unguwar suka fara kallon-kallo, zuciyar Aunty Zaituna ta yi baqiqqirin saboda b'acin rai, me ta ke shirin gani ne haka? Ina Munkaila ya kawo su?

Shiru dai ta yi, kar ta fara qorafi da wuri, a irin unguwannin nan na cikin gari akan samu wasu tsilla tsillan gidajen na masu akwai, wataqila irin shi ne za a kai Ihsan din, dan murmushin dole ta yi, driver ne ya tsaya dan sake tambaya, nan da nan kuwa matashin da suka tambaya ya nuna masu wani gida mai jar qofa, duk ta yi tsa-tsa ta qasa, fentin arziqi babu a gidan, wani ashar Zaituna ta saki ta kalli matashin ta ce

"Kai ko dai baka gane inda muke tambayar ka bane?"

Kallon ta ya yi a sheqe, dan kuwa ya ji sanda ta zabga ashar, ya na gama mata kallon tara saura kwata, ya yi gaba abun shi.

Ba su da wani zabin da ya wuce su taka su shiga, in sun shiga sun ji gaskiya.

Cikin nuna kyankyamin unguwar suka isa gidan, sallama suka yi, suka tsaya bakin qofa, gidan suke qarewa kallo, ta ciki an masa fenti kalar blue, sai qofar wani daki da aka qara da pink, aka saka sabuwar qofa.

Gidan share yake qal qal, kamar mutum ya lashi qasa, ko ina cike yake da tsafta, wata matashiyar budurwa ce ta tashi daga gaban murhu, cike da fara'a, ta tarbe su, kwala wa mahaifiyar su kira ta yi.

"Ummaa, Ummaa ku fito ga su sun iso"

"ke yarinya ga su wa? Wai nan ne gidan su Munkaila?"

Murmushi ta yi sannan ta daga kai tare da fadin,

"Eh nan ne, bismillah, ku zo ku fara shan ruwa, sai a nuna maku dakin nata"

"Ban gane ki na kiran daki ba, kamar za mu kawo ajiyar kaza ko akuya, wai anan zan kawo maku qanwa ta ku ke nufi? Nan akurkin? Da sake, ba zai taba yu wa ba mu saida akuya ta dawo tana cinye mana danga ba, inaaaa"

Nan da nan gida ya kaure da qananan maganganu daga bangaren su Zaituna, mahaifiyar Munkailah kuwa mamakin halayyar su ta hana ta magana, wadannan wadanne irin mutane ne?

Sun jima suna surutai tare da leqa dakin da aka nuna aka ce nan Ihsan za ta zauna, ciki da parlour ne, madaidaici, cikin tsananin b'acin rai Zaituna ta ce

"Inaa ba zai taba yuwuwa ba ai a zato na gaishe da uwar shi xa mu yi a bamu dan rakiya, zuwa ainahin gidan da za su xauna, se kawai a kawo mu nan? Kaf gidan mu ba irin wannan dakunan, kai dakin mai gadin gidan mu ya fi wannan girma, to bari ku ji, ba za ta sabu ba bindiga a ruwa, ai daga cin hanjin awaki ake gane kashin mutum zai d'aci, tun da na gan shi ya zo yau ya zo gobe ko 'yar ledar nan da ake kai wa babu, na san za a rina, yarinyar nan ta kafe ta maqale se ta debo mana dangin wahala, gayyar na ayya gayyar tsiya, to ba zai yu ba, wannan aure.... "

"... Ba zai faru ba, kwarai kin yi gaskiya, mu talakawa ne, kuma muna masu gode wa Allah, duk talaucin mu, bamu taba xuwa roqo ba, muna fafutukar neman na kammu, yaro da babba a gidannan ba mai xaman banza, kowa neman na kai yake, ya rufa wa kan shi asiri, yaro na ya so ya jira ya aurar da qannen shi mata kafin ya yi aure na matsa masa se ya yi aure, na zaba masa yarinyar qawa ta, dake yaran yanxu duk abinda ka kawo sai sun ce ga nasu, ya ce qanwar ku yake so, ina ganin hoton ta na san irin dangin da ta fito daga ciki, amma na hakura saboda na ba shi abinda yake so, ban gajiya da addu'a ba, to alhamdulillahi ba rabon mu kwaso 'yar masu kudi marasa tarbiyya bace, rabon ya auri yarinya daidai da shi ne kyakkyawa ba ragowar man shago ba, ku zo ku tattara ku tafi, maganar aure babu ita, za mu zo mu kwashi kayan mu... Ke maida abincin nan, ai su sun fi qarfin irin wannan,"

Wata budurwa da ke shiga da babban faranti shaqe da snaks da drinks ce ta koma baya, ranta a bace itama saboda rashin mutuncin da su Xaituna suka musu.

Ba tare da ganin girman mahaifiyar Munkaila ba, Zaituna ta zaqe ta na ta ci gaba da zabga rashin mutunci, ba kalar abinda bata kira su da shi ba na talauci da qasqanci.

MAHWISHDonde viven las historias. Descúbrelo ahora